BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Al-Hilal ta kai tayin fan miliyan 120.3 kan Victor Osimhen

Victor Osimhen

Mon, 31 Jul 2023 Source: BBC

Al Hilal ta yi tayin £120.3m ga Napoli kan dan wasan gaba Victor Osimhen, tare da yi wa dan wasan tayin albashin fan miliyan 1 kowane mako.

Tuni kulob din ta Saudi Pro League ta yi tayin Yuro miliyan 300 (£259m) don siyan Kylian Mbappe na Paris St-Germain a bana - duk da cewa dan wasan ya ki ganawa da su - sannan kuma ta yi kokarin sayen Lionel Messi kafin ya koma Inter Miami.

Ana tunanin Napoli za ta so sama da Yuro miliyan 150 kafin ta ma fara nazarin sayar da dan wasan da ya kare a matsayin na daya cikin masu cin kwallaye a gasar Serie A a kakar wasan da ta wuce inda kungiyar ta lashe gasar.

Osimhen, mai shekaru 24, ya kasance daya daga cikinwadanda kungiyar Manchester United ta so daukowa a bazarainda a ahlin yanzu aka samu akasi a tattaunawarsa kan sabon kwantaragi da Napoli.

Sky Italiya ta ba da rahoton cewa wata ganawa tsakanin Napoli da wakilin Osimhen ya kasa samun matsaya kan tsawaita yarjejeniyarsa, wacce za ta kare a bazarar 2025.

Source: BBC