Menu

Al-Ittihad ta naɗa Gallardo sabon kociyanta

37765697 Marcelo Gallardo ya zama mai horar da Al-Ittihad

Sun, 19 Nov 2023 Source: BBC

Tsohon dan wasan tawagar Argentina, Marcelo Gallardo ya zama mai horar da Al-Ittihad, mai buga babbar gasar tamaula ta Saudi Arabia.

Mai shekara 47, ya maye gurbin tsohon wanda ya horar da Wolverhampton da Tottenham, Nuno Espirito Santo.

Tuni dai Gallardo ya amince da ƙunshin yarjejeniyar da za ta kare a ƙarshen kakar 2025.

Ƙungiyar da Gallardo ya horar ita ce River Plate ta Argentina, wadda ta ɗauki kofin ƙasar a ƙarƙashinsa, sannan ya yi kociyan tawagar Uruguay.

Tsohon ɗan wasan tawagar Faransa, Karim Benzema ne kyaftin ɗin Al-Ittihad, wadda ke da tsohon ɗan wasan Liverpool, Fabinho da na Chelsea N'golo Kante.

Yanzu haka ƙungiyar tana mataki na biyar a teburin babbar gasar tamaula ta Saudi Arabia.

An kori Nuno, saboda ƙungiyar ba ta ƙoƙari a kakar nan, an kuma tuntuɓi Julen Lopetegui, wanda ya ce yana jiran dama daga wata ƙungiya a Premier League.

Source: BBC