Sojojin Isra'ila sun kai samame a babban asibitin Gaza, a wani abin da suka bayyana a matsayin wani harin da aka kai wa kungiyar Hamas.
Wani ganau a asibitin Al-Shifa ya shaida wa BBC cewa sojoji sun shiga asibitin cikin dare suna yi wa mutane tambayoyi.
A ranar Laraba, Isra'ila ta ce ta gano "cibiyar aiki" ta Hamas a asibitin, inda ta wallafa hotunan makaman Hamas.
Hamas ta musanta cewa tana gudanar da aiki a cikin babban asibitin, kuma BBC ba za ta iya tabbatar da ikirarin ko wane bangare ba.
Babban jami'in jin ƙai na Majalisar Dinkin Duniya, Martin Griffiths ya ce ya firgita da harin da Isra'ila ta kai, yayin da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce "ta damu matuƙa" ga marasa lafiya da ta rasa hanyar sadarwa da su.
BBC tana tuntuɓar ɗan jarida da wani likita a cikin asibitin don jin abin da ke faruwa a can, yayin da kuma rundunar tsaron Isra'ila (IDF) ita ma take bayar da bayanai.
An bayar da rahoton cewa, rundunar sojin Isra'ila ta buƙaci dukkan maza masu shekara 16 zuwa 40 su bar cikin ginin asibitin zuwa harabar asibitin, amma ban da sassan tiyata da na taimakon gaggawa.
Sojoji sun yi ta harbi a iska domin tilasta wa waɗanda suka rage a cikin asibitin fitowa, inji Khader.
Sai dai Muhammad Zaqout, daraktan asibitocin ma'aikatar lafiya ta Gaza da Hamas ke gudanarwa, ya shaida wa Al Jazeera cewa "babu harsashi ko ɗaya" da aka harba - saboda "babu masu nuna turjiya kuma babu wanda aka tsare" a cikin asibitin.
A cikin wani faifan bidiyo na tsawon mintuna bakwai, mai magana da yawun hukumar ta IDF, Jonathan Conricus, ya nuna kyamarorin tsaro da ya ce an rufe su, da kuma makaman da ya ce bindigogi ƙirar AK47 ne da aka boye a bayan na’urar daukar hoton MRI.
Har yanzu BBC ba ta iya tantance faifan bidiyon ko inda yake ba.
Amma idan Isra'ila ba ta da wani karin bayani, aikin da sojoji suka yi a cikin asibitin bai samu manyan makaman yaƙi ba, in ji wakilin BBC a birnin Kudus Orla Guerin.
Hamas ta san Isra'ila za ta shiga asibitin, don haka, da a ce suna da cibiyar gudanar da ayyukansu a asibitin, da sun san yadda za su yi su kauce musu ta babbar hanyar ƙarƙashin ƙasa ta Gaza.
Gidan rediyon sojojin Isra'ila ya ruwaito cewa har yanzu sojojin ba su sami wata alama ko daya daga cikin mutane 240 da kungiyar Hamas ta yi garkuwa da su ba a harin da aka kai Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba, inda aka kashe wasu mutum 1,200.
Mamayar asibitin Al-Shifa ya zo ne jim kadan bayan da Amurka ta fito fili ta goyi bayan ikirarin Isra'ila cewa Hamas na ajiye kayanta a ƙarƙashin babban asibitin.
Sai dai Dr Ahmed Mokhallalati, wani likita a Al-Shifa, ya shaida wa BBC cewa fararen hula ne kawai a asibitin.
Ya ce akwai ramukan karkashin ƙasa a kowane gini a Gaza ciki har da asibitin Al-Shifa.