Menu

Alkalan da za su busa Premier League mako na 33

Hoton alama

Tue, 25 Apr 2023 Source: BBC

An bayyana dukkan raflin da za su yi alkalancin wasannin mako na 33 a gasar Premier League da za a fara tun daga ranar Talata.

Za a buga wasa uku ranar Talata da karawa hudu ranar Laraba a karkare da fafatawa uku ranar Alhamis.

Kawo yanzu an buga wasa 314, an ci kwallo 876, kuma Erling Haaland na Manchester City shine kan gaba mai 32 a raga.

Jerin wasannin mako na 33 a Premier League:

Ranar Talata 25 ga watan Afirilu

  • Wolverhampton da Crystal Palace


  • Aston Villa da Fulham


  • Leeds United da Leicester City


  • Laraba 26 ga watan Afirilu

  • Nottingham Forest da Brighton


  • Chelsea da Brentford


  • West Ham United da Liverpool


  • Manchester City da Arsenal
  • Ranar Alhamis 27 ga watan Afirilu

  • Everton da Newcastle United


  • Southampton da Bournemouth


  • Tottenham da Manchester United


  • Kawo yanzu Arsenal tana matakin farko a teburi mai maki 75, City wadda take ta biyu mai maki 70 tana da kwantan wasa biyu.

    Newcastle United mai kwantan wasa daya tana ta uku da maki 59 iri daya da na Manchester United ta hudu mai kwantan wasa biyu.

    Wadanda suke karshen teburi sun hada da Everton ta 18 mai maki 28 da Nottingham Forest ta 19 mai maki 27, sai Southampton ta karshe mai maki 24.

    'Yan wasan da ke kan gaba a cin kwallaye a Premier League:

  • Erling Haaland Manchester City 32


  • Harry Kane Tottenham Hotspur 24


  • Ivan Toney Brentford 19


  • Mohamed Salah Liverpool 16
  • Gabriel Martinelli Arsenal 15


  • Marcus Rashford Manchester United 15


  • Ollie Watkins Aston Villa 14


  • Bukayo Saka Arsenal 13


  • Martin Odegaard Arsenal 12


  • Miguel Almiron Newcastle United 11


  • Callum Wilson Newcastle United 11


  • Aleksandar Mitrovic FC Fulham 11


  • Rodrigo Leeds United 11


  • Jerin alkalan da za su busa wasan mako na 33 a Premier League:

    Talata 25 ga watan Afirilu

  • Wolverhampton da Crystal Palace
  • Rafli: Robert Jones. Mataimaka: Adrian Holmes, Wade Smith. Mai jiran ko-ta-kwana: Bobby Madley. VAR: Peter Bankes. Mataimakin VAR: Marc Perry.

    Aston Villa da Fulham

    Rafli: Thomas Bramall. Mataimaka: Derek Eaton, Steven Meredith. Mai jiran ko-ta-kwana: Andy Madley. VAR: Tony Harrington. Mataimakin VAR: Natalie Aspinall.

  • Leeds United da Leicester City


  • Rafli: Paul Tierney. Mataimaka: Neil Davies, Scott Ledger. Mai jiran ko-ta-kwana: Michael Salisbury. VAR: Stuart Attwell. Mataimakin VAR: Constantine Hatzidakis.

    Laraba 26 ga watan Afirilu

  • Nottingham Forest da Brighton


  • Rafli: Jarred Gillett. Mataimaka: Lee Betts, Richard West. Mai jiran ko-ta-kwana: Anthony Taylor. VAR: Robert Jones. Mataimakin VAR: Adam Nunn.

  • Chelsea da Brentford


  • Rafli: Andy Madley. Mataimaka: Harry Lennard, Nick Hopton. Mai jiran ko-ta-kwana: Simon Hooper. VAR: John Brooks. Mataimakin VAR: Timothy Wood.

  • West Ham da Liverpool


  • Rafli: Chris Kavanagh. Mataimaka: Simon Bennett, James Mainwaring. Mai jiran ko-ta-kwana: Andy Davies. VAR: Neil Swarbrick. Mataimakin VAR: Darren Cann.

  • Manchester City da Arsenal


  • Rafli: Michael Oliver. Mataimaka: Stuart Burt, Ian Hussin. Mai jiran ko-ta-kwana: Craig Pawson. VAR: David Coote. Mataimakin VAR: Eddie Smart.

    Alhamis 27 ga watan Afirilu

  • Everton da Newcastle


  • Rafli: Andre Marriner. Mataimaka: Marc Perry, Nick Greenhalgh. Mai jiran ko-ta-kwana: Graham Scott. VAR: Chris Kavanagh. Mataimakin VAR: Sian Massey-Ellis.

  • Southampton da Bournemouth


  • Rafli: Darren England. Mataimaka: Dan Cook, Dan Robathan. Mai jiran ko-ta-kwana: John Brooks. VAR: Andy Madley. Mataimakin VAR: Harry Lennard.

  • Tottenham da Manchester United


  • Rafli: Anthony Taylor. Mataimaka: Gary Beswick, Adam Nunn. Mai jiran ko-ta-kwana: Thomas Bramall. VAR: Simon Hooper. Mataimakin VAR: Steven Meredith.

    Source: BBC