Sam Allardyce ya bar Leeds United bayan jagorantar ƙungiyar a wasanni huɗu kafin ta nutse ta koma buga gasar Championship.
Mai shekaru 68 ,ya yi rashin nasara a wasa uku sannan ya buga canjaras a biyu lokacin da ya maye gurbin Javi Garcia a ranar 3 ga watan Mayu.
Leeds ta shafe kakar wasa uku a gasar Premier kafin ta gamu da wannan cikas ɗin.
"Na ji dadin jagorantar Leeds United, babbar ƙungiya ce mai magoya baya da dama," in ji Allardyce.
Shugaban Leeds United Angus Kinnear ya ce "muna godiya ga Sam da namijin ƙoƙarin da ya yi domin taimakonmu."
Ƙungiyar ta ce za ta sanar da sabon koci a makonnin da ke tafe.