BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Amurka ta sa lokacin ficewa daga Afghanisatan

 118046215 10d9641f 1f86 4483 Af8b 47589a294a92 Amurka za ta janye dukkanin sojojinta daga Afghanistan inji Shugaba Biden

Thu, 15 Apr 2021 Source: BBC

Amurka za ta janye dukkanin sojojinta daga Afghanistan nan da zuwa ranar goma sha daya ga watan Satumba, shekara ashirin daidai ke nan da al-Qaeda ta kai mata harin tara ga watan Satumba a New York da Washington.

Fadar gwamnatin Amurkar ta ce nan gaba a yau Laraba Shugaba Biden, zai sanar da yadda za a kwashe dakarun daki-daki, daga yakin da ya kasance mafi tsawo da kasar ta yi. Sai dai matakin na shan suka daga 'yan jam'iyyar Republican

Gwamantin shugaba Biden ta fitar da wannan sanarwa ne, ta janye dakarun kasar daga Afghanistan din, bayan wannan dogon yaki na shekara ashirin,, bayan da ta tabbata cewa kungiyar Taliban da gwamnatin Afghanistan za su halarci zaman tattaunawar zaman lafiya kan rikicin Afghanistan din.

Harin wanda ita Amurkar ke jagoranta, da za a yi a Turkiyya nan gaba a cikin wannan wata na Afrilu.

Sai dai shugaban marassa rinjaye a majalisar dattawan Amurkar Mitch McConnel bai yi wata-wata ba wajen fito ya bayyana matukar fargabarsa da kuma sukar matakin wanda 'yan jam'iyyarsa ta Republican ke ganin sam-sam bai dace ba.

Saboda kamar wata raguwar dabara ce, kasancewar akwai sauran aiki kuma ja da suke gani;

Mitch McConnel ya ce: ''Janye dakarun Amurka da kadan-kadan daga Afghanistan babban kuskure ne. Ja da baya ne a wurin abokin gabar da ba a riga an murkushe ba, kaucewa daga jagorancin Amurka.

Shugabanni daga jamiyyun biyu, da suka hada da dani, sun yi suka lokacin da gwamnatin da ta gabata ta kawo shirin kasassabar janyewa daga Syria da Afghanistan. Saboda haka wadannan muryoyi a wadannan jam'iyyu biyu, dole ne a yanzu ma su kara nuna damuwa a kan sanarwar ta gwamnatin Biden a yau.

McConnel ya kara da cewa, 'kasassabar janyewa irin wannan, za ta yi watsi ta bar kawayenmu na yanki da Afghanistan da kuma na kungiyar tsaro ta NATO, a yakin ta'addancin da muke yi tare, wanda ba mu kai ga nasara ba tukuna.

Kuma ma zai yi watsi ne musamman da matan Afghanistan, wadanda 'yanci da kuma hakkinsu na daidaiku za su kasance cikin hadari.''

Source: BBC