BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

An ci tarar Kano Pillars naira miliyan daya

21276138 Yan wasan Kano Pillars | Hoton alama

Wed, 25 Oct 2023 Source: BBC

An ci tarar Kano Pillars naira miliyan daya, bayan magoya bayanta sun shiga fili a karawar mako hudu da Rivers United.

Ita kuwa Heartland ta Owerri an gargade ta, kuma an umarce ta a kan ta ja kunnen magoya bayanta, sannan ta shirya bita don koya musu dabi'ar goyon baya ba tare da nuna gaba ba.

Tun ranar Litinin ne, hukumar shirya gasar Firimiya ta Najeria ta dau matakin hukunta Pillars da jan kunnen magoya bayan Heartland.

An samu Pillars da laifi ne, sakamakon haura wa cikin fili da magoya bayanta suka yi domin murnar kwallon da suka ci a minti na 93 a Sani Abacha Stadium.

Hukumar ta kuma ce abin da magoya bayan Heartland suka yi a wasan na mako na hudu na tare 'yan wasa da alkalan karawar a cikin fili bayan tashi daga wasan, abu ne da bai kamata ba.

An bukaci magoya bayan Heartland su zamo masu da'a, sannan su rungumi halayya ta goyon baya ba tare da gaba ba.

Source: BBC