Menu

An cinye gidan ubana a caca - kociyan Swansea

91817319 Kociyan Swansea City, Russell Martin

Sun, 16 Apr 2023 Source: BBC

Kociyan Swansea City, Russell Martin ya ce ba zai taba manta ranar da aka cinye gidan ubansa a caca ba, lokacin yana da shekara takwas da haihuwa.

Saboda haka yana cike da murna da Premier ta zartar da hukuncin kungiyoyin da ke buga gasar da su cire tallan caca a gaban rigunansu da suke buga gasar.

Martin, tsohon mai tsaron bayan tawagar Scotland ya ce yin caca masifa ce, ya kuma ga yadda ta kassara abokan taka ledarsa wadanda ke yin ta.

''Ba na kaunar caca ko kadan, ina kyamarta,'' in ji Martin.

''Lokacin da aka cinye gidan ubanmu a caca sai komawa wani wuri muka yi mara sukuni, sakamakon da mahaifina ya kamu da yin caca ta tsiya.''

''Za kayi murna ranar da kaci kudi mai yawa a caca - amma idan ta juya maka baya ka dinga tafka asara kenan, wanda kullum za ka yi ta sa ran za ka ci wasa amma ina har sai an cinye komai naka kafin ka farga.''

An cimma matasaya cewar dukkan kungiyoyin da ke buga Premier League za su cire sakon tallata caca a rigunansu na gasar tamaula zuwa karshen kakar 2025-26.

Idan wa'adin ya cika kungiyoyin da ke fatan ci gaba da tallata caca, za su iya yi a hannun riguna ko a allon da ke gefen filin wasa.

Kawo yanzu kungiyoyi takwas ne a Premier League ke yi wa kamfanin caca tallace tallace a rigunansu kan kudi da ya kai £60m a kowacce kakar tamaula.

Ita kanta Swansea, kungiyar da Martin ke horarwa tana talla caca a rigunanta.

Source: BBC