BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

An dakatar da Al Nasr daga sayen ƴan wasa kan bashin Ahmad Musa

Ahmed Musah

Thu, 13 Jul 2023 Source: BBC

Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya Fifa ta yanke hukuncin dakatar da ƙungiyar Al Nassr ta ƙasar Saudiyya daga sayen ‘yan wasa har sai ta biya bashin da Leicester City ke bin ta kan Ahmed Musa.

Leicester, wacce ta siyar da dan wasan na Najeriya a shekarar 2018, ta shigar da ƙara kan kuɗin da take bin Al Nassr, fan 390,000.

Kungiya Al Nassr ta yi suna ne a duniya bayan ta dauki Cristiano Ronaldo a bara.

Fifa ta ce "Za a dage haramcin nan da nan bayan an daidaita lamarin basussukan da ƙungiyoyin biyu suka tabbatar."

Al Nassr ta ƙara dan wasan Croatia Marcelo Brozovic a cikin 'yan wasanta a kakar wasa ta bana, kuma ana alaƙanta ta da niyyar biyan makudan kuɗaɗe don siyan Hakim Ziyech na Chelsea.

Source: BBC