BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

An dakatar da magoyin bayan Fulham saboda waƙoƙin ɓatanaci ga ƴan luwaɗi

Hoton firimiya

Thu, 13 Jul 2023 Source: BBC

An dakatar da wani mai goyon bayan kungiyar kwallon ƙafa ta Fulham daga wasan kwallon kafa na tsawon shekaru uku bayan da ya amsa laifin da ya shafi rera wakokin da ke muzanta ’yan luwadi.

Josiah Norman, mai shekaru 25, daga Brixton, ya amsa laifinsa a Kotun Majistare ta Westminster kan laifin da ya faru a lokacin da Fulham ta kara da Chelsea a Stamford Bridge a watan Fabrairu.

Wasan tasakanin ƙungiyoyin biyu ya ƙare ne 0-0.

Ƙarar da aka shigar ta biyo bayan hukuncin da aka yanke a watan Janairun 2022 da Ma’aikatar Shari’a ta Crown ta yanke inda aka ayyana wata waƙa wadda galibi ake yi wa ‘yan wasan Chelsea da magoya bayanta a matsayin batanci ga yan luwadi.

Hukumar kwallon kafa ta Ingila kuma a yanzu za ta iya hukunta kungiyoyi idan magoya bayansu suka rera waƙar.

An kuma kama magoya bayan Wolves da Liverpool da laifin rera waƙoƙin ɓatanci ga 'yan luwadi da ake zargin an yi a wasannin da suka yi da Chelsea a bara.

Yayin da Manchester City, da Manchester United da kuma Nottingham Forest duk suka yi Allah wadai da rahotannin cewa magoya bayansu sun rera waƙoƙin da ke muzanta 'yan luwadi a wasannin da suka buga da Chelsea.

Source: BBC