Menu

An fara cire rai kan yiwuwar sake tsagaita wuta a Gaza

46616733 Hoton alama

Mon, 11 Dec 2023 Source: BBC

Firaministan Qatar, Sheikh Mohammed bin Abdulrahman al-Thani, ya bayyana a birnin Doha cewa, hare-haren bama-bamai da Isra'ila ke yi a zirin Gaza na rage yiwuwar cimma wata sabon sulhu.

Ya tabbatar da aniyar Qatar ta matsa wa bangarorin biyu lamba domin tsagaita wuta.

Qatar ta taka rawar gani a tattaunawar tsagaita buɗe wuta na tsawon mako guda a watan Nuwamba, inda ta taimaka wajen sako mutanen da aka yi garkuwa da su.

A halin da ake ciki, firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce a ranar Lahadi "yaƙin yana ci gaba".

Ya ce a cikin 'yan kwanakin nan "'yan ta'addan Hamas da dama" sun mika wuya, kuma suna "ajiye makamansu suna mika kansu ga jarumanmu".

"Wannan shi ne farkon karshen Hamas," in ji shi.

Kalaman na zuwa ne a daidai lokacin da wahalhalun da ake fuskanta a Gaza ke ƙara ƙazancewa.

A ranar Lahadi da yamma, hukumar lafiya ta Hamas a Gaza ta ce an kashe kusan Falasɗinawa 18,000 a yanzu.

A wani sakon murya da ya aika wa tashar talabijin ta Aljazeera, reshen mayaƙan Hamas ya ce tsagaita buɗe wuta na wucin-gadi ya tabbatar da sahihancinsa, kuma ba za a sake kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su ba har sai Isra'ila ta shiga tattaunawa.

Bugu da kari, Abu Ubaida ya kuma ce mayakan Hamas sun lalata gaba daya ko wani bangare na motocin sojin Isra'ila 180 tare da kashe "adadi mai yawa" na sojojin Isra'ila, kuma har yanzu tana ci gaba da kai wa Isra'ila hari, kuma "abin da zai zo a gaba zai fi muni".

A taron da aka yi a birnin Doha, shugaban hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Falasɗinawa (UNRWA), Philippe Lazzarini, ya ce yankin ya zama "jahannama a duniya" kuma "lalle wannan shi ne yanayi mafi muni da na taɓa gani".

Shi ma da yake jawabi a wajen taron, firaministan Falasɗinawa, Mohammad Shtayyeh ya ce "bai kamata a bar Isra'ila ta ci gaba da keta dokokin jin-kai na ƙasashen duniya ba", ya kuma yi kira da a kakaba mata takunkumin ƙasashen duniya.

Shtayyeh dai yana wakiltar hukumar Falasɗinawa ne, kungiyar da ke aiki a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan, wadda ta ke da bambanci da gwamnatin Hamas da ke a Gaza.

A lokacin da taron ke gudana birnin Doha, a kudancin Gaza ana ci gaba da gwabza fada.

Birnin Khan Younis, wurin da aka ce mutane su koma don guje wa faɗan da ake yi a arewacin ƙasar, yanzu haka yana fuskantar hare-haren bama-bamai - inda Isra'ila ke neman fararen hula da su fice daga tsakiyarsa.

Da yake magana da BBC, babban mashawarcin Isra'ila, Mark Regev, ya ce za a yi "yaƙi mai wuya" a Khan Younis, kuma ya buƙaci fararen hula da su yi "kaura zuwa yankuna masu aminci" - tare da isar tankokin Isra'ila zuwa tsakiyar birnin a yammacin Lahadi.

An dai ɗauki hoton fararen hula a birnin suna tattara gawarwaki yayin da suke jimamin ƴan'uwansu da aka kashe.

Da aka tambaye shi kan halin da ake ciki a yankin da Isra'ila ta kira yankunan da ke da tsaro, Regev ya ce ƙasarsa ta yi iyakacin kokarinta na kare rayukan fararen hula.

A baya an shawarci fararen hula a Gaza da su yi tafi zuwa "yanki mai aminci" a al-Mawasi. Yana auna nisan kilomita 8.5 (kilomita 3.3), yankin ƙarami ne idan aka kwanatat da Filin jirgin sama na Heathrow na London, yana da ƴan gine-gine kuma galibi ya ƙunshi dunƙulen yashi da ƙasar noma.

A halin da ake ciki, Isra'ila kuma ta tsunduma cikin harkokin diflomasiyya - tana kira ga kawayenta da bin dabaru daban daban

"A ɗaya ɓangaren ba za ku iya goyon bayan kawar da ƙungiyar Hamas da kuma matsa mana lamba kan kawo karshen yaƙin ba, wanda zai hana kawar da Hamas," a cewar Netanyahu yayin da yake ganawa da majalisar ministocinsa.

Yana magana ne kwanaki biyu bayan ƙasashe 13 na Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya sun goyi bayan wani kudiri na tsagaita bude wuta cikin gaggawa, inda Amurka ta ki amincewa da matakin sannan Birtaniya ta kaurace.

Isra'ila ta kuma musanta ikirarin da shugaban hukumar ta UNRWA Mr Lazzarini ya yi na cewa tana kokarin tilastawa 'yan Gaza ficewa daga yankin da kuma shiga cikin Masar - wani abu da kafafen yaɗa labaran Isra'ila suka ruwaito a baya.

Hukumar lafiya ta duniya ta kuma ɗauki matakin da ba a saba gani ba na zartar da wani kuduri da ke neman a kai tallafin gaggawa ta ɓangaren lafiya zuwa Gaza, inda a baya babban daraktan ta ya kira halin da ake ciki a yankin "mummunan bala'i".

Source: BBC