Menu

An fitar da jadawalin La Liga 2023/24: Getafe da Barca, Athletic da Real

Yan wasan Barcelona

Thu, 22 Jun 2023 Source: BBC

Za a fara kakar tamaula ta La Liga ranar Juma'a 11 ga watan Agusta, sannan a ƙarƙare karawar makon farko ranar Asabar da Lahadi 13 ga watan.

Barcelona ce ta lashe kofin kakar da ta wuce, wadda aka tsara cewar za ta je gidan Getafe.

Ƙungiyoyi uku ne suka samu gurbin shiga La Liga daga ƙaramar gasar Sifaniya a ciki har da Granada da Las Palmas da kuma Deportivo Alaves

Real Madrid, wadda ta yi ta biyu a La Liga za ta je gidan Ahletic Club a wasannin makon farko, Atletico Madrid da sabuwar ƙungiya, Granada.

Ƙungiyoyin da suka bar La Liga a kakar da ta wuce su ne Real Valladolid da Espanyol da kuma Elche.

Sevilla, wadda ta lashe Europa League tana gida, domin fuskantar Valencia.

Kawo yanzu ba a fayyace ranakun da ƙungiyoyin za su kara a tsakaninsu ba, illa dai an fitar da ranar fara La Liga da jadawalin makon farko.

Wasannin makon farko a La Liga 2023/24

  • Almería da Rayo Vallecano
  • Athletic Club da Real Madrid


  • Atlético Madrid da Granada


  • Celta da Osasuna


  • Sevilla da Valencia


  • Las Palmas da Real Mallorca


  • Getafe da Barcelona


  • Villarreal da Betis


  • Real Sociedad da Girona
  • Cádiz vs Alavés


  • Za a kammala La Liga ranar Lahadi 26 ga watan Mayun 2024, ranar da za a buga karawa 10.

  • Almería vs Cádiz


  • Celta da Valencia


  • Getafe da Real Mallorca


  • Girona da Granada


  • Osasuna da Villarreal


  • Rayo Vallecano da Athletic
  • Real Sociedad da Atletico Madrid


  • Sevilla da Barcelona


  • Real Madrid da Betis


  • Las Palmas da Alavés


  • Ranakun da za a buga El Clasico a kakar 2023/24 a La Liga

    Barcelona da Real Madrid za su fara karawa a El Clasico a kaka mai zuwa a Montjuic, filin da Barcelona ta koma a karawar mako na 11 a makon 29 ga watan Oktoba.

    Real Madrid za ta karɓi baƙuncin Barcelona a wasan mako na 32 a La Liga a Santiago Bernabeu a makon 21 ga watan Afirilun 2024.

    Ranakun da za a yi hutu a La Liga kakar 2023/24

    4 ga watan Satumba zuwa 12 ga watan Satumbar 2023

    9 ga watan Oktoba zuwa 17 ga watan Oktoban 2023

    13 ga watan Nuwamba zuwa 21 ga watan Nuwambar 2023

    18 ga watan Maris zuwa 24 ga watan Maris din 2024

    Source: BBC