Menu

An gano alamun sassan jikin mutum a tarkacen jirgin ruwan da ya tarwatse

Jirgin ruwan na sunduki da ke tafiya a karkashin teku

Fri, 30 Jun 2023 Source: BBC

Jami'an tsaron gabar tekun Amurka sun ce an gano alamun abin da ake kyautata zaton wani sashe ne na jikin dan'Adam, daga tarkacen karamin jirgin ruwan nan na sunduki na karkashin teku, wanda ya yi hadari dauke da mutum biyar a cikinsa, suka mutu.

Jirgin na Titan ya bace tun ranar Lahadi 18 ga watan Yuni 2023, ba a san abin da ya faru da shi ba sai ranar Alhamis, kwana hudu bayan da ya shiga teku, a kan hanyarsa ta zuwa ganin mushen katafaren jirgin ruwan nan na Titanic da ke karkashin tekun Atalantica, wanda ya yi hadari a shekarar 1912.

A yanzu ƙwararrun jami'an lafiya na Amurka za su gudanar da bincike da nazari a kan abubuwan da aka gano da ake ganin sashe ne na jikin dan'Adam, a jikin tarkacen jirgin da aka gano.

A sanarwar da hukumar rundunar jami’an tsaron gabar tekun Amurkar ta fitar dangane da wannan abu da aka gano ta ce kwararrun ma’aikatan lafiya na Amurka za su gudanar da cikakken bincike a kai.

A yanzu kwararrun masu bincike na nazari a kan tarkacen jirgin ruwan na sunduki da aka gano can a karkashin teku ba nisa daga inda mushen katafaren jirgin ruwan na Titanic.

Masu binciken daga hukumomi daban-daban na duniya na kokarin gano abin da ya haddasa hadarin ne domin hana sake aukuwarsa a gaba.

Jami’an tsaron na Amurka sun ce har yanzu akwai gagarumin aiki da za a yi domin gano dalilin hadarin da kuma kare maimaicinsa.

Ana dai ci gaba da lalubo karin tarkacen jirgin tare kuma da tattaunawa da ji daga bakin wadanda ke da alaka ko hannu a kan bulaguron jirgin ruwan na Titan, kafin kuma a gudanar da wani binciken na jama’a kan hadarin.

Ana ganin jirgin ruwan na ya tarwatse ne a kusan lokacin da aka daina jin duriyarsa, minti 90 bayan ya nutsa cikin teku inda ya fara wannan tafiya.

Mutum biyar da ke cikinsa su ne shugaban kamfanin jirgin da ya shirya bulaguron, Stockton Rush mai shekara 61, da attajirin Birtaniya mai yawon bude idanu na ganin kwakwaf Hamish Harding, mai shekara 58.

Sauran su ne attajiri dan Birtaniya asalin Pakistan Shahzada Dawood, mai shekara 48, da dansa Suleman Dawood, mai shekara 19, da kuma kwararren mai ninkaya Bafaranshe Paul-Henry Nargeolet, mai shekara 77.

Source: BBC