BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

An haifi jariri da jinin iyaye uku karon farko a Birtaniya

Hoton alama

Wed, 10 May 2023 Source: BBC

Hukumar kula da ƙwayayen haihuwar al'umma a Birtaniya ta tabbatar da haifar wani jariri ta hanyar amfani da ƙwanduwar ƙwayoyin halittun iyaye uku karon farko a ƙasar.

Jaririn na da mafi yawan gudan halittun gado (DNA) daga iyayensa biyu, sai kuma ƙasa da kashi ɗaya daga wata mace da ta bayar da gudunmawar ƙwanduwar ƙwan halittarta.

Fasahar da aka fara amfani da ita a karon farko, wani yunƙuri ne na kare haihuwar yara da cutukan ƙwanduwa wato ''mitochondria'' a ƙwayoyin halitta waɗanda jarirai kan yi gado daga iyayensu musamman mata.

An haifi jarirai a ƙalla biyar ta irin wannan hanya, amma ba a fitar da wani ƙarin bayani ba.

Ba a iya warkar da cutukan ƙwanduwar ƙwayoyin halittu, kuma suna iya janyo mutuwa cikin ƴan kwanaki ko ma sa'o'i bayan haihuwar jariri.

Wasu iyalai sun yi asarar 'ya'ya da yawa, amma ana ganin wannan fasaha a matsayin zaɓi ɗaya tilo da ta rage musu wajen samun lafiyayyun yara.

'Mitochondria' wasu 'yan mitsi-mitsin abubuwa ne a cikin ƙwayoyin halittun ɗan'adam da ke markaɗa abinci don samar da sinadaran ƙara kuzari.

Ƙwanduwar da ke da matsala na gaza ƙara kuzarin jiki kuma sukan haifar da matsalar ƙwaƙwalwa da lalacewar tsokar jiki da ciwon zuciya har ma da makanta.

Ana gadon waɗannan matsaloli ne daga wajen uwa kawai.

Don haka, tsarin warkar da cutukan ƙwanduwa ta hanyar samun gudunmawa daga wata matar daban, wani sabon nau'in ƙyanƙyasar ƙwan haihuwa a ɗakin bincike (IVF) ne, ta hanyar amfani da ƙwanduwa daga lafiyayyen ƙwan wata.

Akwai fasahohi guda biyu na ba da gudummawar ƙwanduwar ƙwayar halitta. Hanya ta farko, ana yi ne bayan ƙwayayen haihuwar uwa sun haɗu da maniyyin uba, sannan na biyun, ana yi ne kafin ƙyanƙyashe ƙwan.

Sai dai ƙwanduwar na da irin nasu bayanan gado ko gudan halittun gado na DNA, abin da ke nufin jaririn da aka haifa zai yi gadon gudajin halittun gado daga iyayensu, da kuma wasu gudajin halittun gado ƙalilan daga wadda ta ba da gudunmawa. Wannan wani canji ne na dindindin da iyaye za su gadarwa 'ya'yansu zuri'a bayan zuri'a.

Wannan tsarin ba da gudunmawar gudan halittar gado (DNA) yana da tasiri ne kawai wajen samar da lafiyayyiyar ƙwanduwa, amma ba ya shafar wasu siffofi, kamar kamanceceniya, kuma bai zama wani tsari da za a iya kira "mahaifa uku" ba.

An soma aiwatar da wannan tsari a Newcastle, kuma an bijiro da dokoki domin bayar da damar samar da irin waɗannan jarirai a Birtaniya a 2015.

Sai dai, Birtaniya ba ta yi saurin ci gaba da aiwatar da fasahar ba.

Jaririn farko da aka haifa ta wannan fasaha, shi ne na wasu iyalai ƴan Jordan da suka je ganin likita Amurka a 2016.

Hukumar kula da Ƙwayayen Haihuwa da 'Yan tayi ta ce jarirai a ƙalla biyar aka haifa da irin wannan fasaha ya zuwa 20 ga watan Afrilun 2023.

Ba ta ba da haƙiƙanin alƙaluman ba saboda ɓoye sirrin iyalan.

Taƙaitattun bayanan sun ɓulla ne bayan da jaridar Guardian ta nemi ƙarin haske a ƙarƙashin dokar ƴancin samun bayanai.

"Rahoton cewa an haifi wani adadi na jarirai ɗauke da ƙwanduwar gudunmawa a Birtaniya wani ci gaba ne, a wani lamari da mai yiwuwa zai kasance cikin taka tsantsan kuma a hankali na kimantawa da sake fasalin ba da gudunmawar ƙwanduwar ƙwan halitta," in ji Sarah Norcross, Daraktar Gidauniyar Progress Educational Trust.

Babu dai wani bayani daga ayarin jami'an Newcastle, don haka har yanzu akwai rashin tabbas a kan ko aikin ya yi nasara.

Farfesa Robin Lovell-Badge daga cibiyar nazari ta Francis Crick ya ce "Zai zama abin ban sha'awa, sanin yadda fasahar sauya ƙwanduwa ta gudana a aikace, ko jarirai sun kuɓuta daga cutukan da suka danganci ƙwanduwar ƙwan halitta ko kuma akwai yiwuwar su fuskanci wani hatsari nan gaba a rayuwarsu."

Akwai yiwuwar aiki zai iya "komawa baya" idan wata ƙwanduwar ƙwan halitta mai matsala, ta hayayyafa kuma ta yi sanadin haddasa wata cuta.

An taɓa ƙiyasin cewa, ana iya haifar jarirai kusan 150 ta wannan hanya, duk shekara a Birtaniya.

Source: BBC