BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

An hallaka sama da mutum arba'in a gidan yari a Honduras

Hoton alama

Wed, 21 Jun 2023 Source: BBC

Shugabar Honduras, Xiomara Castro, ta bayyana kaduwarta game da abin da ta kira kisan gillar da aka yi wa sama da mutane arba'in a wani gidan yarin mata a yayin wani artabu tsakanin wasu gungun kungiyoyi da ba sa ga maciji da juna.

Shugabar ta ce ba shakka, za ta tuhumi shugabannin tsaron kasar kan lamarin, wanda ya janyo kafa dokar-ta-baci.

Rahotanni sun ce daya daga cikin kungiyoyin daurarrun ne suka garkame wasu abokan gabarsu a dakinsu, sannan suka cinna musu wuta.

An rika sanya hotunan bidiyon da aka yada a shafukan sada zmunta sun nuna bakin hayakin da ya turnuke na tasowa daga kurkukun.

Ana ganin fursunoni ashirin da biyar sun kone kurmus, sannan kuma aka harbe wasu.

Tazarar da ke tsakanin gidan yarin na Tamara da babban birnin kasar Teguti-yalpa, ba ta wuce kilomita talatin ba.

Mataimkiyar ministar tsaro ta kasar Julissa Villanueva, ta ayyana dokar ta-baci tare da alkawarin gudanar da gagarumin bincike a kan tashin hankalin.

Ms Villanueva, ta ce ba za a lamunta da asarar rayukan.

Ba a dai san ko dukkanin wadanda suka mutu a rikicin fursunoni ba ne, a gidan da ke da mutum kusan 900..

Delma Ordóñez, wadda ke wakiltar iyalan fursunonin

Wata da ke wakiltar iyalan fursunonin ta gaya wa manema labarai cewawani sashen ginin ya lalace gaba daya.

A shekarar da ta wuce Shugaba Xiomara Castro, ta ce za ta dauki tsauraran matakai na yaki da kungiyoyin bata-gari.

Ms Villanueva ta ce za a gudanar da bincike tare da gurfanar da wadanda ke da hannu a gaban kotu.

Honduras ta yi suna wajen tashin hankalin kungiyoyin yan daba da bata-gari, abin da ya haddasa yawan kisan kai.

Kasar tare da makwabtanta El Salvador da Guatemala, hanyoyi na safarar miyagun kwayoyi daga Latin Amurka zuwa Amurka.

Sannan tana da tarihin rikicin gidan yari da ake alakantawa da kungiyoyin bata-gari.

Akalla mutum 18 aka kashe a 2019 a rikin yan daba a gidan yarin birnin Tela mai tashar jirgin ruwa, da ke arewacin kasar.

Source: BBC