BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

An hango wani ƙaton rami a kan duniyar rana

85302202 Hoton alama

Mon, 11 Dec 2023 Source: BBC

Wani wawakeken rami wanda girmansa zai iya dauke duniyarmu guda 60 ya bude a kan duniyar rana, kamar yadda masana kimiyya suka ce.

Ramin, wanda aka hango yankin da ya bude ya yi duhu, wanda a turance ake kira coronal hole, ya bude ne a kan doron kwallon ranar.

An tsinkayi wannan rami ne daga wata cibiyar lura da sararin samaniya ta Hukumar bincike kan sararin samaniya ta Amurka (NASA), tsakanin ranakun 2 da 4 ga wannan wata na Disamba.

Irin wadannan ramuka da kan faru a kan doron rana ba kamar ramuka ne irin na duniyarmu ba, sai dai wani yanki ne na jikin duniyar ranar da kan zamo ba ya da tsananin zafi kamar sauran bangarorinta.

Irin wadannan yankuna kan zamo sun yi duhu idan aka hango su ta na’urar dauko hoton duniyoyi, inda za a ga cewa sauran bangarori na rana wadanda ke da cikakken zafi su kuma sun yi haske kuma sun fi cunkushewa.

Me ya sa ake samun ramuka a duniyar rana?

Ita dai rana tamkar wane makeken mayen karfe ne.

Kuma ta samu ne daga wani abu da a turance ake kira ‘plasma’, wanda shi kuma wani irin burbushin iskar gas ne mai tsananin zafi, ta yadda kwayoyin zarran da suka taru suka hada shi kan rika rarrabuwa amma suna zagayawa a wuri guda.

A lokacin da wadannan ‘yan mitsi-mitsin kwayoyin suke zagayawa cikin sauri sosai sai su samar da wani yanayi da ke janyo abubuwa zuwa jikinsu, ta haka ne sai su cure su sake komawa cikin kwallon duniyar rana.

To amma yankin da ake samun irin wadannan ramuka su ne inda karfin maganadisun mayen karfen ya ki komawa cikin kwallon duniyar rana.

A maimakon haka sai karfin nasu ya tunkudo zuwa wajen duniyar rana, wato zuwa cikin sararin samaniyarta.

Wannan na nufin ke nan tsananin zafi a irin wadannan yankuna da kuma cunkushewar iskar gas din kan ragu idan aka kwatanta da saura.

Sai dai duk da cewa ana yawan ganin irin wadannan ramuka na budewa a kan rana, to ba wani abin tashin hankali ba ne, sannan idanunmu kadai ba za su iya hango ramukan ba kai tsaye (sai da taimakon na’ura).

Ba a san tsawon lokacin da wannan rami zai ci gaba da kasancewa ba a kan duniyar rana, amma masana kimiyya sun ce irin wadannan ramuka kan iya kasancewa har tsawon juyawa daya na duniya, wato kwana 27.

Kuma ana sa ran cewa yankin da aka hango wannan sabon rami a kan duniyar rana zai juya daga bangaren da ke fuskantar duniyarmu nan da ba da jimawa ba.

Source: BBC