BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

An kama mutumin da ya illata mutum-mutumin da ke gaban ofishin BBC

Hoton Alana

Sun, 21 May 2023 Source: BBC

An kama wani mutum bayan da aka zarge shi da illata wani mutum-mutumi mai cike da cece-kuce a wajen hedikwatar BBC da ke birnin Landan da guduma.

An kira ƴan sanda a ranar Asabar, inda aka ba su rahoton cewa wani mutum ya hau saman gini da ke wajen ofishin BBC kuma yana lalata mutum-mutumin Eric Grill.

An yi ta kiraye-kirayen cewa a cire shi saboda wanda ya zana shi yana cin zarafin 'ya'yansa mata a cikin rubuce-rubuce.

Wannan dai shi ne karo na biyu da aka yi niyyar cire mutum-mutumin wanda aka saka a 1930.

An sauko da mutumin daga saman wurin da ya hau jim kadan bayan karfe 6:00 na yamma.

Rundunar ‘yan sandan birnin Landan ta ce an kama shi ne bisa zarginsa da laifin lalata mutum-mutumin kuma za a kai shi ofishin ƴan sanda.

Hakan na zuwa ne bayan wani mai zanga-zangar ya ɗauki guduma tare da far wa wurin da mutum-mutumin yake a watan Janairun bara, inda har yanzu ana ci gaba da gyare-gyare daga ɓarnar da aka yi a lokacin da lamarin ya faru.

A tsawon ranar Asabar, ana iya ganin wani mutum a kan tarkace sanye da abin rufe fuska yana yi wa jami’an da ke kasan wurin ihu.

Hotuna sun kuma nuna yadda ya bugi mutum-mutumin da guduma.

An saka wani katafaren shinge, kuma da farko 'yan sanda sun ce ba zai yiwu a tsare mutumin ba, duba da yanayin yadda lamarin ya faru.

Sun kara da cewa kwararrun jami’ai na halartar wurin da lamarin ya faru.

An haife Gill a shekara ta 1882, ya zama ƙwararren mai zane wanda aikinsa ya haɗa da zana manyan mutum-mutumi a kan gine-ginen da ke tsakiyar Landon, ciki har da na cocin Westminster da kuma ainihin hedkwatar ƙarƙashin ƙasa ta birnin Landan.

Shi ne kuma ya ƙera Gill Sans, wani nau'in Ingilishi da aka fi amfani da shi mai suna British typeface.

Gill ya mutu a shekara ta 1940, amma a cikin 1989 an buga wani littafi na tarihi rayuwa wanda ya ba da cikakken bayani kan cin zarafin da aka yi wa 'ya'yansa mata guda biyu, dangantaka da 'yar uwarsa, da kuma jima'i da aka yi da karensa.

Mutum-mutumin da ke wajen ofishin BBC, wanda aka assasa a 1933, ya ƙunshi haruffan Prospero da Ariel daga wasan kwaikwayon Shakespeare na The Tempest.

Editan al'adu na BBC Katie Razzall ta ce "Gill ya kasance babban nasara kuma sanannen mai zana mutum-mutumi" wanda aikinsa ya haifar da tambayoyi "game da ko za ku iya yanke hukunci ga mai zane ko wani bisa la'akari da ainihin rayuwarsa ko kuma a kan fasaharsa ta zane".

A baya BBC ta ce an kammala aikin gyaran ɓarnar da aka yi wa mutum-mutumin a bara a ranar 19 ga watan Yuni. Hakanan akwai shirye-shirye don sanya wata lamba kusa da mutum-mutumin don sanar da batun tarihinsa.

Hukumar ta ce lamarin na baya-bayan nan al'amari ne na ‘yan sanda da hukumar ba da agajin gaggawa.

Source: BBC