BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

An kama tsohon shugaban Amurka a hukumance

Tsohon shugaban Amurka, Donald Trump

Tue, 4 Apr 2023 Source: BBC

Tsohon shugaban Amurka, Donald Trump ya isa wata kotu a unguwar Lower Manhattan, inda a hukumance aka kama shi bisa zargin aikata laifi.

Trump ya ɗaga wa magoya bayansa hannu kafin ya shiga cikin ginin kotun tare da rakiyar jami'an tsaron farin kaya.

Akwai ɗumbin 'yan jarida da 'yan kallon da suka yi dandazo a gaban ginin da tsakar ranar a birnin New York.

Ana zargin tsohon shugaban ne da biyan wata mai fina-finan batsa, Stormy Daniels toshiyar baki don kada ta yi bayani game da alaƙar nema da ke tsakaninsa da ita a lokacin da yake neman takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2016.

Muna tafe da ƙarin bayani........

Source: BBC