Menu

An kashe allunan talla a Bagadaza bayan haska bidiyon batsa

52231243 Tutar Iraki

Mon, 21 Aug 2023 Source: BBC

Jami'ai a birnin Bagadaza na Iraƙi sun yi umarnin a kashe duk wani allon talla da ke gefen titi a birnin biyo bayan wani fim ɗin batsa da masu kutse suka sanya a ɗaya daga cikin allunan.

Wannan lamari ya faru ne a ɗaya daga cikin manyan titunan babban birnin ƙasar ta Iraƙi.

An ta yaɗa wannan bidiyo a kafafen sada zumunta na ƙasar da wajenta.

'Yan sanda sun ce sun kama wani mutum da ake zargi da hannu cikin wannan lamari.

Sanarwar 'yan sandan ta ce wanda ake zargi mai lura da na'urori ne da yake da matsalar kuɗi da kamfanin da yake sanya talla a allunan.

Rahotanni sun ce, mutumin ya sanya bidiyon ne a matsayin wani mataki na ramuwa.

Mai kutsen "sa sanya bidiyon na mintina da dama kafin daga baya mu katse mutar allon" a ranar Asabar, kamar yadda wani jami'n tsaro da ya nemi a sakaa sunansa ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Wannnan "halayyar rashin ɗa'ar ta sanya hukumomi kashe duka wani allon talla da ke titin birnin Bagadaza" saboda da duba yadda lamarin ya faru.

A safiyar ranar Lahadi aka kashe duka wutar allunan da ke birnin, waɗanda yawanci suke haska tallan kayayyaki ko kuma na 'yan siyasa.

Source: BBC