Menu

An kashe fiye da mutum 130 a harin Burkina Faso

 118813870 Gettyimages 1198467333 Maharan sun kona gidaje da wata kasuwa yayin harin da su ka kai kan kauyen Solhan

Mon, 7 Jun 2021 Source: BBC

Wasu mahara dauke da muggan makamai sun kashe fiye da mutum 132 a wani hari da su ka kai a wani kauye da ke arewacin Burkina Faso, hari irinsa mafi muni a shekarun da su ka gabata inji gwamnatin ƙasar.

Maharan sun kona gidaje da wata kasuwa yayin harin da su ka kai kan kauyen Solhan.

Babu kungiyar da ta dauki alhakin kai harin, amma masu ikirarin jihadi sun dade su na kai hare-hare a cikin kasar, musamman a yankunan da ke kan iyaka.

Shugaban Majalisar Dinkin Duniya ya ce harin ya tayar ma sa da hankali.

Antonio Guterres ya ce "Ina yin Allah wadai da wanan harin da ya kara bayyana bukatar kasashen duniya su kara kaimi domin taimakawa kasashen da ke yakar masu yadaakidar kiyayya da rasa rayuka masu yawa.

Jami'an tsaron kasar na can su na farautar maharan.

Shugaban kasar Roch Kabore ya sanar da kwanaki uku na zaman makoki, wanda ya wallafa a shafin Twitter, yana cewa "tilas mu hada kai domin yakar hadakar miyagu".

A wani harin na daban da aka kai cikin daren Juma'a, an kashe mutum 14 a kauyen Tadaryat wanda ke da nisan kilomita 150 arewa da Solhan.

A watan jiya, mutum 30 aka kashe a gabashin Burkina Faso.

Source: BBC