Firaministan Isra`ila Benjamin Netanyahu ya shafe daren da ya gabata a asibiti, a dalilin abin da aka ce rashin isasshen ruwa a jiki.
Ofishinsa ya ce an dage taron da ya saba yi na mako-mako a ranar Lahadin nan har sai washegari, Litinin, duk da cewa Netanyahun ya bayyana cewa ya wartsake.
Wannan shi ne karo na biyu da ake kwantar da shi a asibiti ya shafe dare, a cikin wata tara.
A watan Oktoba an kwantar da shi a asibiti inda ya shafe dare, sakamakon jigata da ya yi bayan ya yi azumi.
Ofishinsa ya takaita bayanai kan maganar kwantar da shi a asibitin, illa dai kawai an bayyana cewa shugaban gwamnatin ya rika jin jiri.
Kuma binciken farko ya nuna cewa yana fama ne da rashin isassen ruwa a jiki, kamar yadda aka bayar da bayani.
Netanyahun ya bayyana a wani hoton bidiyo yana tsaye yana murmushi, inda ya ce ya samu kansa a cikin wannan matsala ne a dalilin bulaguro da suka yi da iyalinsa zuwa tekun Galilee.
Ya ce, ya kasance a cikin rana ba hula ba kuma ruwa.
Isra'ila tana fama da tsananin zafin da ake fama da shi yanzu haka a kudancin Turai da wasu sauran kasashen duniya, musamman na bangaren arewaci.
Mista Netanyahu, wanda ke da shekara 73 a duniya yana jagorantar gwamnatin Isra'ila mafi tsananin ra’ayin rikau da rashin sassauci a tarihin kasar.
Haka kuma yana fuskantar shari'ar cin hanci da rashawa, zargin da ya musanta.
Bugu da kari yana fama da zanga-zangar kin jinin gwamnatinsa, da kuma tashin hankali mafi muni a cikin shekaru a yankunan da Isra'ila ta mamaye na Falasdinawa.