BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

An raba gari tsakanin Ajax da koci Maurice Steijn

75647763 Hoton alama

Wed, 25 Oct 2023 Source: BBC

Kungiyar Ajax da kocinta, Maurice Steijn sun raba gari, bayan wata hudu da ya yi a kan aikin.

Mai shekara 49 ya koma Ajax daga Rotterdam a watan Yuni kan yarjejeniyar kaka uku.

To sai dai kungiyar ba ta kokari a bana, wanda ta lashe kofin gasar Netherland karo 36 tana ta biyun karshe da maki biyar, bayan wasa bakwai da ta buga.

Steijn da mahukuntan Ajax sun amince kowa ya kama gabansa, bayan taro da suka yi a tsakaninsu sau biyu ranar Litinin.

Kawo yanzu Ajax ta sanar da mataimakin koci, Hedwiges Maduro zai yi aikin rikon kwarya.

Wasa biyu kacal Ajax ta yi nasara daga 11 a dukkan fafatawa karkashin Steijn, wanda ya horar da ADO Den Haag, da VVV-Venlo da kuma NAC Breda.

Erik ten Hag ya ja ragamar Ajax ta lashe kofin Netherlands uku a jere kafin ya koma Manchester United a 2022, yayin da aka kori wanda ya maye gurbinsa Alfred Schreuder a Janairun 2023.

Kocin rikon kwarya, John Heitinga shi ne ya ja ragamar Ajax a bara, wadda ta yi ta uku a teburin gasar kasa, daga nan ya koma West Ham United a matakin mataimakin David Moyes.

Source: BBC