BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

An sauya ranar da Arsenal za ta fafata da Everton a Premier

Martin Odegaard

Wed, 6 Sep 2023 Source: BBC

Mahukuntan Premier League sun sauya ranar da Everton za ta karɓi baƙuncin Arsenal, bayan da Gunners za ta buga Champions League.

Tun farko an tsara Arsenal za ta je Goodison Park buga wasan mako na biyar ranar Asabar 16 ga watan Satumba, yanzu ya koma 17 ga watan nan.

Arsenal za ta buga Champions League a kakar nan ranar Laraba 20 ga watan Satumba da za ta kara da PSV Eindhoven a Emirates.

Gunners mai maki 10 bayan wasa hudu tana ta na mataki na biyar a teburin Premier League, ita kuwa Everton mai maki daya tana ta 18 a kasan teburi.

Kimanin wasa shida aka sauya ranakun bugawa bayan da ƙungiyoyinsu ke cikin gasar Zakarun Turai ta 'Champions League' ko Europa League ko kuma Conference League.

Wasannin da aka sauya ranakun bugawa a Premier League:

Asabar 16 ga watan Satumba

  • Newcastle da Brentford


  • Lahadi 17 ga watan Satumba

  • Everton da Arsenal


  • Lahadi 24 ga watan Satumba

  • Chelsea da Aston Villa


  • Lahadi 8 ga watan Oktoba

  • Wolves da Aston Villa


  • Asabar 21 ga watan Oktoba

  • Sheff Utd da Man Utd
  • Lahadi 29 ga watan Oktoba

  • Aston Villa da Luton


  • Source: BBC