BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

An wanke tsohon ɗan wasan Manchester City, Mendy daga zargin fyaɗe

Benjamin Mendy

Fri, 14 Jul 2023 Source: BBC

Kotu ta wanke tsohon ɗan wasan Manchester City, Benjamin Mendy daga zargin yi wa wata mata fyaɗe da kuma yunƙurin yi wa wata matar ta daban fyaɗen.

Ɗan wasan mai shekara 28, an zarge shi da far wa wata mata mai shekara 24 a gidansa da ke yankin Cheshire a Birtaniya, cikin watan Oktoban 2020.

An kuma zargi Mendy da ƙoƙarin yi wa wata matar ta daban mai shekara 29 fyaɗe, inda ta ce ya ci zarafinta a gidan nasa, shekara biyu da suka gabata.

Hakan na zuwa ne bayan wanke shi daga zarge-zarge shida na fyaɗe a watan Janairu.

Ɗan wasan, ɗan asalin Faransa ya fashe da kuka a lokacin da aka karanta hukuncin cewa ba a kama shi da laifi ba.

Source: BBC