BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

An yi kazamin dambe tsakanin Dan Aliyu da Manun Garkuwa

51123235 Yan wasan Dambe

Sun, 17 Dec 2023 Source: BBC

An buga dambe da yawa a ajon Autan na Aisha a Marabar 'Nyanya gidan wasa na Idris Bambarewa da ke 'yan tifa a jihar Nasarawa, Najeriya.

Cikin damben da aka yi har da wanda aka sa zare tsakanin Dan Aliyu da Manu Shagon Garkuwa da suka yi turmi daya mai kyau aka raba su.

Alhaji Zurmi ne ya raba wasan, wanda ya yi wa 'yan damben biyu alheri daga baya ya ce su hakura, bayan da suka yi kazamin dambe ba kisa.

Da yake wasannin na ajon Autan na Aisha ne, wanda ya dauki watanni bai fadi ba a Maraba, kungiyar Guramada ta bai wa dan wasan naira 500,000 kamar yadda suka sanar.

Daga nan ne aka sa damben naira 50,000 tsakanin Ushu Shagon Inda da Manu Shagon Garkuwa, kuma turmi biyu suka yi ba a samu gwani ba.

Wasannin da aka buga guda daya ne daga ciki aka yi kisa, wanda Shagon Bisi ya kashe Shagon Yalo.

Sauran sakamakon wasannin da aka yi canjaras:



  • Shagon Nokiya da Shagon na Jimama
  • Shagon Autan dan Bunza da Shagon Bahagon Buma
  • Garkuwan Duna da Dogon Awilo
  • Shagon Yahaya da Bahagon Yahayan Tarasa
  • Dogon Mamman da Shagon Yahayan Tarasa
  • Ilele Shagon Garkuwan mai caji da Bahagon Ali Kawoji
  • Dogon Awilo da Shagon Autan dan Bunza


Source: BBC