BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

An yi rana mafi tsananin zafi a tsawon shekara 60 a China

Hoton alama

Thu, 22 Jun 2023 Source: BBC

Birnin Beijing na shan zafi mafi tsanani da aka taɓa gani a watan Yuni cikin fiye da tsawon shekara 60, inda ma'aunin mercury ya kai selsiyas 41.1C, a cewar hukumomin kula da yanayi na ƙasar China.

Birnin yana fuskantar dogon yanayin zafi mai tsanani kuma lamarin zai ci gaba har zuwa ƙarshen watan Yuni.

A ranar Alhamis, jami'ai sun ce ita ce rana mafi tsananin zafi a watan Yuni tun da aka fara taskace bayanai a 1961.

Tsawon watanni da dama an fuskanci zafi mai tsanani bana cikin ƙasar China, lamarin da ya janyo fargabar samun ƙarancin makamashi.

A watan jiya, Shanghai birni mafi girma a ƙasar, da yawan mutane kimanin miliyan 25 a gaɓar tekun gabashi, ya fuskanci rana mafi zafi cikin watan Mayu a tsawon ƙarni.

Akwai mutane sama da miliyan 21 da ke zaune a Beijing, babban birnin ƙasar a ɓangaren arewa.

A ranar Alhamis, wata tashar bin diddigin yanayi a birnin ta ba da rahoton cewa zafi ya kai maki 41.8 a ma’aunin salsiyas.

Tun da farko hukumomi sun ankaras da mutane cewa rana za ta buɗe ta yi launin ruwan goro, gargaɗin yanayi na kusa da mafi tsananin zafi, inda suka ce yanayin na iya kai wa salsiyas 39 a cikin ‘yan kwanakin nan har zuwa Asabar.

Ofishin kula da yanayi na ƙasa ya kuma fitar da jan hankali a makon jiya game da yiwuwar samun matsanancin zafi - mako biyu kafin yadda zafin ya saba sauka a shekarun baya.

Hukumomi a Beijing da Tianjin da kuma sauran birane a arewaci da gabashin China, sun shawarci mutane su jingine fita zuwa aiki waje a lokacin da rana ta fi ƙwallewa kuma su nemi taimakon lafiya matuƙar suka fuskanci larurorin da akan yi fama da su a yanayin matsanancin zafi.

Wasu kuma sun gargaɗi mutane da cibiyoyin kasuwanci a kan su taƙaita amfani da lantarki.

A makon jiya, Hukumar kula da Makamashi ta Ƙasa ta aiwatar da atisayen ko-ta-kwana irinsa na farko a yankin gabashin China, inda suka kwatanta halin da za a iya shiga a lokacin da aka samu ƙaruwar wutar lantarki da kuma a lokacin da aka samu gagarumar ɗaukewar lantarki.

Yanayin na iya kasancewa "akasari mai tsanani" bisa la'akari da harkokin tsaron babban layin lantarki, a cewar hukumar.

A birnin Tianjin mai gaɓar ruwa, ƙarin buƙatun wutar kunna na'urar sanyaya ɗaki ya sa lodi ya ƙaru a kan babban layin lantarki da kashi 23% a bara.

Ma'aikata a ofishin samar da lantarki sun riƙa sintiri a hanyoyin ƙarƙashin ƙasa kullum don tabbatar da cewa wayoyin lantarki na aiki yadda ya kamata, a cewar jami'ai.

Source: BBC