Menu

An yi wa Robertson tiyata a allon kafaɗa - Klopp

13006969 Andy Robertson

Wed, 25 Oct 2023 Source: BBC

Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya ce an yi wa mai tsaron bayan ƙungiyar, Andy Robertson tiyata a allon kafaɗa sakamakon raunin da ya ji lokacin da yake yi wa Scotland wasa.

Robertson ya ji rauni ne a lokacin da ya yi taho-mu-gama da mai tsaron ragar Sifaniya, Unai Simon a cikin watan nan a karawar neman shiga Euro 2024.

''An yi masa tiyata kuma cikin nasara kamar yadda ya kamata, '' kamar yadda Klopp ya sanar da manema labarai.

''Ban san ranar da zai murmure ba, amma dai an ɗauki matakin farko.''

Robertson ya buga wasa takwas da cin kwallo ɗaya a Liverpool a kakar nan, an sauya shi da Kostas Tsimikas a karawar hamayya ta Merseyside da Everton.

Tsimikas, mai shekara 27, ya buwa wa Liverpool Europa League da LASK Linz da na Union Saint-Gilloise da EFL Cup a fafatawa da Leicester City a kakar nan.

An kuma sauya shi a league da Liverpool ta doke Bournemouth.

Liverpool za ta fafata da kungiyar Faransa, Toulouse a Anfield a Europa League ranar Alhamis.

Source: BBC