Menu

An yi wa golan PSG Donnarumma fashi a Paris

Gianluigi Donnarumma da abokiyar zamansa

Fri, 21 Jul 2023 Source: BBC

An kai wa golan Italiya da Paris St-Germain, Gianluigi Donnarumma da abokiyar zamansa hari tare da yi masa fashi a gidansu da ke birnin Paris.

Wasu gungun mutane ne suka kai harin inda suka ɗaure su a gidansu da ke gunduma ta takwas a tsakiyar babban birnin kasar, kamar yadda majiyar 'yan sanda ta shaida wa kafar yada labaran Faransa.

Daga nan ne ɗan wasan da abokiyar zamansa suka tsere zuwa wani otal da ke kusa bayan maharan sun tafi.

Ma’aikatan otal ne suka sanar wa 'yan sanda kafin aka kai su asibiti.

Kakakin ofishin mai shigar da kara na birnin Paris ya shaida wa BBC cewa, "An fara bincike kan zargin yin fashi da makami da wata kungiya da ta shirya ta kuma gudanar cikin dare a gidan Mista Donnarumma."

Rahotannin da ba a tabbatar da su ba a shafin yada labarai na Actu17 sun ce maharan sun yi awon gaba da kayan ado da agogo da kuma kayan alatu da kudinsu ya kai Yuro 500,000 (£430,000).

Dan wasan ya samu rauni kadan yayin da abokiyar zamansa, Alessia Elefante, bai samu rauni ba, kamar yadda majiyoyi suka shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Faransa.

Ofishin mai shigar da kara ya ce rundunar ‘yan sandan kasar Faransa ta musamman ta BRB da ke da alhakin yaki da fashi da makami, ya fara gudanar da bincike.

Gianluigi Donnarumma, mai shekaru 24, ya koma Paris ne shekaru biyu da suka wuce, kuma a ranar Juma'a ne ake sa ran zai hade da tawagar Paris St-Germain gabanin wasan sada zumunta na farko da kulob din za ta buga da Le Havre da kuma rangadin kasashen Japan da Koriya ta Kudu.

Ba shi ne dan wasan kwallon kafa na PSG na farko da ‘yan daba ke kai wa hari ba, amma galibin hare-haren da aka kai a baya an yi su ne yayin da wanda aka kai ma harin ba su gida.

A watan Janairun da ya gabata, an yanke wa wasu maza biyu hukuncin dauri a gidan yari sakamakon wani hari da su ka kai a watan Maris din 2021 a gidan dan wasan kwallon kafar Brazil Marquinhos da ke Yvelines a yammacin birnin Paris.

Marquinhos yana wasa a lokacin da lamarin ya faru amma mahaifinsa yana gidan tare da 'ya'yansa mata guda biyu. An bugi mahaifin a fuska da kuma hakarkarinsa amma bai ji rauni ba.

Kuma har ila yau a wannan ranar ce aka yi wa gidan abokin wasan Marquinhos Angel Di Maria fashi.

Source: BBC