Menu

An yi wa malamar jinya ɗaurin rai da rai bisa laifin kashe jarirai a Birtaniya

31945773 Lucy Letby mai shekara 33

Mon, 21 Aug 2023 Source: BBC

An yankewa Lucy Letby mai shekara 33, hukuncin ɗaurin rai-da-rai.

An yanke mata hukunci ne bayan samun ta da laifin kashe jariri bakwai, da kuma yunƙurin kashe ƙarin shida a wani asibitin yara da ke Countess of Chester.

Ana bayyana ta a matsayin wadda ta fi kowa halaka jarirai a tarihin Birtaniya.

An tuhumi ma'aikaciyar jinyar da yi wa jariran allura, ba tare da cire iska a cikin ruwan magani ba, sannan ta sanya wa wasu jarirai guba a cikin sinadarin insulin.

Bayan yanke mata wannan hukunci, Lucy Letby ba ta nuna wata alamar nadama ba.

A yazu dai Letby za ta shafe tsawon gaba ɗayan rayuwarta a tsare, inda ta zama mace ta huɗu a Birtaniya da aka taɓa yankewa irin wannan hukunci, wanda shi ne mafi tsanani da ake yankewa mai laifi.

Alƙalin kotun Mai shari'a Goss, ya bayyana laifin da Lucy ta aikata a matsayin "babban abin ƙyama".

Ya ce "ta aikata abin da ya saɓa da tunanin ɗan'adam mai cikakken hankali, da ya san kimar lura da jarirai, kuma babbar cin amanar waɗanda suka yarda da aikin ma'aikatan lafiya ne".

Alƙalin ya bayyana ta a matsayin maras tausayi, wadda ke sanya damuwarta cikin aikinta.

Lauyan da ke kare ta, Ben Myers KC, ya ce "tun bayan fara shari'ar Lucy ta ƙi musanta aikata laifin da ake zargin ta da aikatawa, dangane haka ba shi da wani mataki da zai ɗauka da zai iya kai wa ga rage tsawon hukuncin da aka yanke mata".

Harabar kotun ta cika maƙil da iyayen da ma'aikaciyar jinyar ta halaka wa jarirai, har ma wasu sun yi sharɓar hawaye a lokacin da alƙalin yake karanta hukuncin da ya yanke wa mai laifin.

Source: BBC