Babbar gasar kwallon ƙafa ta ƙasar Saudiyya ka iya zama "ɗaya daga cikin manyan gasa biyar a duniya" idan har aka ɗauko manyan ƴan wasa a duniya, in ji ɗan ƙwallon Portugal, Cristiano Ronaldo.
Ana jijitar cewa Lionel Messi da Karim Benzema da Luka Modric za su koma murza leda a Saudiyya kuma Ronaldo ya ce yana "maraba" da zuwansu.
Gwarzon ɗan kwallon duniya har sau biyar ya koma Al Nassr ne a watan Disamban bara.
Yarjejeniyarsa da United za ta ƙare ne a shekara ta 2025.
A halin yanzu Paris St-Germain ta tabbatar da cewa Messi zai bar ƙungiyar a wannan bazarar kuma ɗan ƙwallon na Argentina, mai shekaru 35 ya kasance jakadan yawon buɗe ido na ƙasar Saudiyya.
Ronaldo ya zura ƙwallo 14 a cikin wasa 16 inda ya taimaka wa ƙungiyarsa Al Nassr ta kammala gasar a matsayin ta biyu a kan tebur a yayin da Al Hilal ta lashe gasar.