BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

'Ana daƙile mata a siyasar Najeriya'

Catriona Laing, Jakadiyar Burtaniya a Najeriya, Catriona Laing ta ce ana danne mata a harkokin siyasa

Wed, 29 Mar 2023 Source: BBC

Jakadiyar Birtaniya a Najeriya Catriona Laing ta ce an ƙi bai wa mata a ƙasar damar da ta kamata wajen ganin sun bayar da gudummawa domin ci gaban ƙasar.

Catriona Laing ta bayyana haka ne lokacin wata tattaunawa ta musamman da BBC, inda ta kuma nuna damuwa kan raguwar yawan matan da aka zaɓa ko bai wa muƙaman siyasa a gwamnatin Najeriya.

Ta lura da cewa yawan matan da suka samu nasarar cin zaɓe zuwa majalisar tarayya a zaɓen da aka kammala, ya ragu matuka idan aka kwatanta da zaɓen 2019.

Ta ce hakan ya mayar da Najeriya baya a ɓangaren siyasa.

Mrs Laing wadda ta kasance a Najeriya tsawon shekara biyar, ita ce mace ta farko a matsayin jakadiyar Birtaniya zuwa Najeriya.

Ta ce Najeriya tana matsayi na 123 cikin ƙasashe 126 a duniya a ɓangaren daidaiton jinsi, wani abu da ta nuna takaicinta a kai.

Catriona ta ce duk da haka, matan Najeriya da dama na nuna bajinta a ɓagarori daban-daban a faɗin duniya, inda ta ce an ƙi ba su damar shiga siyasa a ƙasarsu.

“Matan Najeriya suna da baiwa daban-daban - sai dai duk da kasancewarsu kashi 50 na al'ummar ƙasar, abin takaici shi ne ba su samun damar bayar da gudummawar da ta kamata a Najeriya," in ji Catriona.

Ta ce ta ga matan Najeriya masu hazaka da basira a ciki da kuma wajen ƙasar, inda ta ce akwai Mataimakiyar Sakatare Janar a Majalisar Dinkin Duniya da shugabar Hukumar Cinikayya ta Duniya (WTO) da kuma wasu da dama da duniya ke alfahari da su.

Source: BBC