BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Ana daf da bayyana makomar Tonali wanda ya karya dokar yin caca

73834917 Dan wasan Newcastle United, Sandro Tonali

Wed, 25 Oct 2023 Source: BBC

Dan wasan Newcastle United, Sandro Tonali ya yi atisaye a safiyar Talata a kungiyar, bayan kusa kammala binciken da ake yi masa game da karya ka'idar yin caca.

Wasu rahotanni na cewar dan wasan mai shekara 23, zai san makomarsa ranar Laraba, kafin wasan Champions League da Newcastle za ta kara da Borussia Dortmund a St James Park, ana cewar za a dakatar da shi ne da kuma cin tara.

Dan wasan ya yi atisaye a Newcastle United, wadda za ta buga wasa na uku a rukuni na shida.

Wakilan Tonali sun kwashe ranar Litinin suna tattaunawa da masu shigar da kara, bayan da ya je buga wa Italiya tamaula a farkon watan nan.

Tonali da Nicolo Zaniolo, wanda ke buga wasan aro a Aston Villa daga Galatasaray na jiran hukuncin da za a dauka a kansu, bayan karya dokar yin caca.

An zargin Tonali, wanda ya koma buga gasar Premier League daga AC Milan, da yankar AC Milan da tsohuwar kungiyarsa, Brescia da kuma yin caca a lokacin da yake buga musu tamaula.

Ya buga wa Newcastle United wasa 11 har da wanda kungiyar ta doke Paris St Germain 4-1 a Champions League a farkon watan nan.

Source: BBC