Menu

Ana gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Jamhuriyyar Tsakiyar Afrika

 117568715 22d617f1 E411 4134 Ab8e Ec08a175411c Za a sake gudanar da wannan zabe ne yau a wurare da dama da aka fuskanci matsala a zaben farko

Sun, 14 Mar 2021 Source: BBC

Ranar Lahadin nan ne 'yan kasar Jamhuriyar Tsakiyar Afirka ke fita rumfunan zaɓe don kaɗa ƙuri'a a zagaye na biyu na zaɓen 'yan majalasar kasar.

Tun dai ranar 27 ga watan Disamba 2020 ne aka gudanar da zaben zagayen farko da ya samu cikas a sanadiyar rikicin da 'yan tawayen kasar suka tayar a wasu wurare.

Za a sake gudanar da wannan zabe ne yau a wurare da dama da aka fuskanci matsala a zaben farko.

Mahukunta sun ce sake gudanar da zaben shi ne zai bayar da damar a tabbatar da wanda ya yi nasara ko bayyana wuraren da aja sany natsala domin yin gyara.

Hukumomin kasar ta Jamhuriyar Tsikar Afirka na da gatan ganin cewa a wannan rana ta lahadi za a gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da lumana ba tare da fargaba ba.

An dai dauki tsauraran matakan tsaro don ganin mahimmancin da wannan zabe ya ke da shi wajen kawo zaman lafiya cikin kasa baki daya.

Hadakar jam'iyu masu akidar kawo sauyi da ta hada da 'yan tawaye, wadanda Majalasar Dinkin Duniya ta yi ammar cewa suna goyon bayan tsahon shugaban kasar Francois Bozize, na barazanar hana gudanar da zaben .

Wannan hadaka dai ita ce ta kawo yamutsin da ya sa aka dakatar da zaben a ranar 27 ga watan Disamba 2020.Kuma wannan abun shi ya sa a wurare da dama ba a gudanar da zaben ba a lokacin da masu kada kuri'a su je domin zaben shugaban kasa da kuma zaben 'yan majalasar dokokin kasar.

Duk da wannan yamutsi da ya gudana, 'yan tawayen sun kasa hana a sake zaben Faustin Archange Touadera a sabon wa'adin zama shugaban kasa .Ya kuma yi nasarar lashe zaben da kashi 53 cikin 100 na kuri'un da aka kada .To sai dai 'yan tawayen har yanzu ba su amince da zaben ba wanda tuni su ka yi fatali da sakamakon.

Yan majalasar 22 kawai aka zabe daga cikin 140 da kasar ta kunsa.

Duk da ikirarin barazanar da 'yan tawayen su ka yin na kawo yamutsi a zaben,hukumomin kasar na cewa an kara daukar matakan tsaro da dama domin ganin zaben ya gudana salum-alum cikin tsanaki da sahihanci.

Source: BBC