Menu

Ana kukan tsadar kaya a Ghana da Najeriya saboda rufe iyakokin Nijar

18380740 Hoton alama

Wed, 9 Aug 2023 Source: BBC

Al'ummar wasu ƙasashen Afirka ta Yamma da ke maƙwabtaka da Nijar suna kokawa a kan ƙarin tsadar wasu kayan abinci saboda takunkuman da Ecowas ta sanya wa ƙasar saboda juyin mulkin sojoji.

A Ghana, 'yan ƙasar na ci gaba da bayyana damuwa kan tashin farashin albasa, yayin da shinkafa take neman gagarar mutane da yawa a wasu yankuna kamar Sokoto, ɗaya daga cikin jihohin Najeriya masu maƙwabtaka da Nijar.

Albasa na cikin manyan amfanin gona da ake Nijar ke nomawa, kuma ƙasar tana fitar da ita zuwa sauran ƙasashen Afirka ta Yamma kamar Togo da Benin da Ghana da Kwatdebuwa har ma da Guinea, yayin da ake safarar shinkafa 'yar waje zuwa ƙasashe kamar Najeriya ta cikin Nijar.

Hamɓarar da gwamnatin Shugaba Mohamed ranar 26 ga watan Yuli ya janyo zazzafan martani daga Ecowas wadda ta lafta wa ƙasar takunkumai.

Takunkuman waɗanda suka haɗar da batun katse alaƙar kasuwanci da ƙasashe wakilan ƙungiyar, ya janyo maƙalewar manyan motocin dakon albasa fiye da 70 a kan iyakar Nijar.

Wani wakilin masu safarar albasa a Accra, Sani Abubakar ya ce halin da ake ciki a Nijar zai yi "matuƙar illa ga harkokin safarar irin waɗannan kayayyaki a kasuwarmu."

Shi kuwa wani dillalin shinkafa a Sokoto, Mallam Abun Audu Mai Ruwa ya shaida wa BBC cewa "Buhu(n shinkafa) mai cin kwano 45 yanzu ya kai N88,000 zuwa N90,000".

Ya ce "tun kafin dambarwar Nijar, farashin shinkafa ya fara tashi, amma takunkumin Ecowas ya ƙara ta'azzara lamarin".

Hauhawar farashin kayan abincin, ya zo ne bagatatan, inda magidanta a Sokoto ke bayyana lamarin da abin firgici da tayar da hankali.

Farashin buhun albasa, wadda fitacciyar abar sarrafa miya ce a gidajen 'yan Ghana mai yiwuwa zai tashi da kashi 90% matuƙar takunkumin ya ci gaba da aiki, in ji 'yan kasuwa.

Ghana na shigar da kusan kashi 70% na albasar da take buƙata daga Nijar a cewar 'yan kasuwar masu dillancin albasa.

A shekarar 2021, Nijar ta fitar da albasar da ta kai darajar dala miliyan 23 zuwa Ghana da sauran ƙasashen Afirka ta Yamma.

Fatan sulhu da sojojin Nijar na ƙara dusashewa

Yunƙurin shiga tsakani a Nijar ya gamu da cikas a ranar Laraba bayan da masu juyin mulkin watan Yuli suka ƙi amincewa da wani ayarin diflomasiyya, yayin da maƙwabtan ƙasashe masu goyon bayan shugabannin mulkin soji suka yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya ta hana auka wa Nijar da ƙarfin soji.

A ranar Talata ne, gwamnatin Nijar ta hana jami'an Majalisar Dinkin Duniya, da na Ecowas da kuma AU sauka a Yamai, a ƙoƙarinsu na bijire wa matsin lambar hawa teburin tattaunawa kafin taron ranar Alhamis da ƙungiyar Ecowas ta kira a birnin Abuja, don tattaunawa a kan yiwuwar amfani da ƙarfi.

Lamarin dai ya dusashen dusashe fatan cimma matsayar diflomasiyya dangane da turka-turkar da ke barazanar ƙara dagula al'amura a yankin Sahel na Afirka ta Yamma - da ke fama da yawan juyin mulki da mummunan rikicin masu ikirarin jihadi.

Kasashen Mali da Burkina Faso da ke maƙwabtaka da Nijar, wadanda su ma suke ƙarƙashin mulkin soja, sun nemi Kwamitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya hana ɗaukar matakin amfanin da ƙarfin soji a kan Nijar.

A cewarsu hakan zai iya haifar da "sakamakon da ba za a iya hasashen ƙarshensa ba” da kuma janyo tarwatsewar ƙungiyar Ecowas.

"Gwamnatocin riƙo a Burkina Faso da Jamhuriyar Mali sun ja hankali kan babban alhakin da ya rataya a wuyan kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya, inda suka buƙaci ya yi amfani da dukkan hanyoyi don hana auka wa ƙasa mai 'yancin cin gashin kai da ƙarfin soji," a cewar wata wasiƙar da ministocin wajen Mali suka buga a shafin X ko Tuwita.

Sun ce sun ɗauki alhakin samar da mafitar diflomasiyya da tattaunawa, amma ba su bayar da cikakken bayani ba.

A baya dai, ƙasashen Mali da Burkina Faso sun ci alwashin cewa za su kia ɗauki don kare Nijar, matuƙar Ecowas ta auka mata, a cewarsu za su yi la'akari da hakan a matsayin shelar yaƙi ne a kansu.

Sakataren wajen Amurka Antony Blinken ya faɗa a ranar Talata cewa ya tattauna da hamɓararren Shugaba Mohamed Bazoum, inda ya bayyana masa ƙoƙarin Amurka na ci gaba da ganin an warware taƙaddamar cikin lumana.

Shugaban Najeriyar kuma jagoran ƙungiyar Ecowas, Bola Tinubu, ya sanya wa Nijar ƙarin takunkumi a ranar Talata da nufin ƙara matsa lamba ga hukumomi da ɗaiɗaikun da ke da hannu a juyin mulkin watan Yuli.

Kungiyar Ecowas ta ce amfani da ƙarfin soji zai zama mafita ta ƙarshe, matuƙar sojojin ba su sauka daga mulki ba, kuma suka ƙi sakin Mohamed Bazoum.

Wace mafita ta rage wa ECOWAS ?

Wasu masharhanta dai sun sun soki lamirin Ecowas a kan barazanar amfani da ƙarfin soji maimakon fifita hanyoyin masalaha da na diflomasiyya don kawo ƙarshe dambarwar juyin mulkin Nijar.

Wani tsohon jami'in diflomasiyya a Najeriya, Ambasada Suleiman Dahiru ya ce bai kamata ana maganar tattaunawa don warware taƙaddamar da ke faruwa cikin lumana ba, amma a fara barazanar ƙaddamar da yaƙi, wanda zai iya harzuƙa shugabannin juyin mulkin.

"Ina jin dalilin da ya sa aka nuna rashin karramawa ga tawagar Najeriya da ta ƙunshi Janar Abdulsalami Abubakar da Mai alfarma Sarkin Musulmi da suka je don tattaunawa da sojojin Nijar, shi ne zazzafan matakin da Ecowas ta ɗauka".

"Rashin girmamawa ne a ce sojojin sun ƙi karɓar Janar Abdulsalami Abubakar da Sultan bisa la'akari da matsayinsu kuma ana girmama su sosai a Najeriya da faɗin duniya," in ji tsohon jakadan.

"Da sojojin sun saurare su, da za a iya samun ƙofar da za a bi ta sasanta wannan lamari."

Ya ce hanyar diflomasiyya dai ita ce mafi dacewa da za a ci gaba da amfani da shi a yunƙurin sasanta irin wannan lamari, amma ba yaƙi ba"

A cewarsa, "Akwai mutanen da ake jin nauyinsu, ba lallai sai 'yan Najeriya ko daga ƙasashen Ecowas ba, da za a iya tura su don ganawa da sojoji a ƙoƙarin sasantawa.

Jakadan ya ce kamata ya yi a ƙara yin taka-tsantsan da wannan lamari saboda dangantakar da ke tsakanin Najeriya da Nijar.

Source: BBC