BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Ana sa ran Arsenal za ta fara wasa da David Raya ranar Talata

76329411 David Raya

Wed, 25 Oct 2023 Source: BBC

Ana sa ran Arsenal za ta fara buga wasa da mai tsaron raga, David Raya ranar Talata a wasanta da Sevilla na gasar Champions League a filin Ramon Sanchez Pizjuan.

Gunners tana amfani da Raya, maimakon Aaron Ramsdale a wasannin da take bugawa cikin 'yan makonnin nan.

To sai dai kuma, ana ganin laifin golan dan kasar Sifaniya, kan sakacin da ya yi a kwallon da Mykhailo Mudryk ya ci a wasan da Gunners ta tashi 2-2 da Chelsea a gasar Premier League.

An tambayi Mikel Arteta ko Raya yana cikin matsin lamba, tun bayan komawarsa Emirates daga Brentford, sai kocin ya ce ''Ni ban ga hakan ba.''

''Wannan shi ne matsin lambar da ake fuskanta idan kana wasa a babbar kungiya, inda ake bukatar nasara da zama kan ganiya, kuma kana da wani dan wasa da kullum so yake ya karbi gurbinka.''

Ramsdale ba ya cikin 'yan wasan Arsenal da suka kara da Chelsea a karshen mako, wanda ya taya matarsa jego, bayan ta haifi da namiji.

To sai dai yana cikin 'yan wasan da Arsenal ta je da su Sifaniya, domin fuskantar Sevilla.

Source: BBC