Watakila Andreas Christense ba zai buga wasa na biyar a El Clasico da za a fafata tsakanin Barcelona da Real Madrid ba.
Dan kwallon ya ji rauni a lokacin da yake buga wa kasarsa tamaula a karshen mako.
Mai tsaron bayan ya fara yi wa Denmark wasan neman gurbin Euro 2024 ranar Alhamis da Finland – amma an canja shi a minti 18 da fara karawar, samakakon rauni.
Bai yi wa kasar karawar da ta je Kazakhstan aka doke ta 3-2 ba ranar Lahadi.
Barcelona ba ta fayyace girman raunin ba, balle ta tantance ranar da zai koma fagen daga, sai daiwasu na cewar zai yi jinyar wata daya.
Idan haka ne kenan ba zai buga wasan Copa del Rey na daf da karshe da Real Madrid ba ranar 5 ga watan Afirilu.
Barcelona ce ta ci wasan farko 1-0 a daf da karshe a Copa del Rey a Santiago Bernabeu.
Haka kuma ba zai yi karawa biyar a La Liga ba, inda Barcelona ke mataki na daya da tazarar maki 12 tsakaninta da Real Madrid ta biyu.