Arsenal ta bayyana cewa ba ta da burin da ya wuce ta kawo dan wasan tsakiyar West Ham Declan Rice a karshe kaka. (Times)
Daraktan wasannin Borussia Dortmund Sebastian Kehl na shirin tattauna wa da Jude Bellingham da iyayensa, game da makomar dan wasan a kungiyar.
Sai dai ya ce ba bu wata kungiya da ta taya matashin dan kwallon Ingilar kawo yanzu. (Kicker)
Dan wasan Gefen Brazil Raphinha da Arsenal ke nema, ya ce ba shida niyyar barin Barcelona a watan Janairu. (Mundo)
Newcastle na kokarin ganin ta sayi dan wasan tsakiyar Chelsea da Ingila Conor Gallagher, da Ruben Loftus-Cheek da kuma Hakim Ziyech na Maroko. (Telegraph)
Daraktan wasanin RB Leipzig Max Eberl ya ce karara take cewa dan wasan gaban Faransa Christopher Nkunku zai tafi Chelsea. ( Bild)
Newcastle da Leicester na rige-rigen sayen dan wasan gaban Fiorentina da Argentina, Nico Gonzalez, kuma kungiyarsa Fiorentina ta Italiya ta ce ba za ta sayar da shi kasa da fam miliyan 40 ba. (TuttoMercatoWeb)
Sai kuma Everton da Newcastle da ke jayayya kan dan wasan Leverkusen da Ecuador, Piero Hincapie, wanda wata majiya tace Tottenham ma na nemansa. (Football Insider)
Leeds United ta kara wani abu kan tayin farko da ta bai wa Angers na fam miliyan 22, kan dan wasan tsakiyarta Azzedine Ounahi, wanda ya taka wa Maroko rawa sosai a gasar kofin duniya. (90 Min)
Chelsea da Tottenham sun daina neman dan wasan gaban Everton da Ingila, Anthony Gordon. (CaughtOffside)
Mai tsaron bayan Faransa William Saliba, ya ce yana jin dadin zama a Arsenal, a daidai lokacin da ake tattauna tsawaita zamansa a Emirates. (Independent)