BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Arsenal na shawaran dauko Kvaratskhelia da Kudus

Georgia Khvicha Kvaratskhelia

Mon, 31 Jul 2023 Source: BBC

An sami rahotannin cewa Arsenal na tunanin yiwuwar dakan dan wasan Napoli da Georgia Khvicha Kvaratskhelia, mai shekara 22.

An gaya mana cewa Arsenal ta sami ƙarfafa ne saboda dangantakar da ke tsakanin ƙungiyar ta London da sabon daraktan wasanni na Napoli, Mauro Meluso.

An fahimci cewa a baya Napoli ta yi watsi da bukatu da suka samu kan Kvaratskhelia daga kungiyoyin Premier League.

Kvaratskheliataka rawar gani a kakar wasan da ta gabata inda Napoli suka ci nasarar lashe gasar Seria A , yayin da ake tunanin shi ɗan wasa ne wanda zai yi tasiri a tsarin wasan Mikel Arteta.

Har ila yau wadansu rahotanni na cewa Arsenal na zawarcin Mohammed Kudus daga Ajax a wannan bazarar bayan sun dauko Kai Havertz da Declan Rice da kuma Jurrien Timber.

Tsohon shugaban Arsenal Sven Mislintat zai iya taka rawar gani a yunkurin da Gunners ke yi na dauko Mohammed Kudus a wannan bazarar yayin da shi ne darektan fasaha na Ajax yanzu.

Daraktan wasanni na Arsenal Edu ya riga ya yi aiki tare da Mislintat don kammala yarjejeniyar Jurrien Timber - kuma yanzu yana iya komawa kan teburin tattaunawa da magajinsa a kokarinsa na dauko Kudus.

Source: BBC