BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Arsenal na son Rice, Saudiyya na zawarcin Mahrez

Dan wasan West Ham da Ingila Declan Rice

Fri, 9 Jun 2023 Source: BBC

Arsenal za ta sake zage damtse a zawarcin ɗan wasan West Ham da Ingila Declan Rice kan fam miliyan 92. (Telegraph - subscription required)

West Ham ta nuna matsuwa kan dauko ɗan wasan Fulham da Portugal Joao Palhinha mai shekara 27, domin maye gurbin Rice. (Mail)

Chelsea ita ma na iya gwada sa'arta kan Rice da kuma ɗan wasan Brighton da Ecuador Moises Caicedo, mai shekara 21. (90min)

Dan wasan Nice da Faransa Khephren Thuram, mai shekara 22, ya amince ya je Liverpool. (Football Transfers)

Mai buga tsakiya a Chelsea da Croatia Mateo Kovacic, mai shekara 29, ya amince da tayin Manchester City bayan tattaunawa mai zurfi. (Fabrizio Romano)

Liverpool za ta tattauna da wakilan ɗan wasan Borussia Monchengladbach mai shekara 22 Manu Kone. (Fabrizio Romano)

Real Madrid na kokarin ganin yadda za ta kammala cinikin Harry Kane kan £68m bayan Tottenham Hotspur taki sayar da ɗan wasan mai shekara 29 ga Manchester United. (Marca - in Spanish)

Newcastle na zawarcin 'yan wasa daga kungiyoyin Leeds United da Amurka, irinsu Tyler Adams, da Harvey Barnes na Leicester City da kuma James Maddison. (Telegraph)

Maddison kuma a yanzu ya kasance wanda sabon kocin Tottenham Ange Postecoglou ke hari. Amma dole kungiyar ta biya sama da £50m kan ɗan wasan. (Telegraph - subscription required)

Ɗan wasan Manchester City da Jamus Ilkay Gundogan, mai shekara 32, ya kasance wanda Paris St-Germain ke zawarci a yanzu. (L'Equipe - in French)

Kungiyar Al Ahli ta Saudiyya na farautar ɗan wasan Algeria Riyad Mahrez daga Manchester City. (Fabrizio Romano)

Dole Tottenham ta kara kuɗaɗen tayin da take gabatarwa na £20m kan mai tsaron raga na Sifaniya David Raya. (i Sport)

Arsenal na nazari kan ɗan wasan Sifaniya mai shekara 18 Ivan Fresneda da ke buga La Liga a Valladolid. (Football London)

Leicester City na duba yiwuwar tsohon mai horas da Aston Villa Steven Gerrard bayan faɗawa rukunnin 'yan dagaji a Firimiya. (Mail)

Zinedine Zidane ya yi watsi da tayin aikin koci daga PSG domin maye gurbin Christophe Galtier. (Le Parisien - in French)

Tottenham za ta bukaci Juventus ta rage kuɗi £35m da ta sa a cinikin Dejan Kulusevski mai shekara 23. (Nicolo Schira)

Shugaban kungiyar Shakhtar Donetsk, Sergei Palkin ya yi barazanar kai Tottenham karar muddin ta yi kokarin saye ɗan wasansu mai shekara 23 Manor Solomon, da ke zaman aro a Fulham. (ESPN)

Manchester United na nazari kan tura ɗan wasanta mai shekara 21 Mason Greenwood zaman aro a Turai. (Mail)

Source: BBC