BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Arsenal na son dauko David Raya, Chelsea ta matsa kan Mbappe

David Raya

Mon, 31 Jul 2023 Source: BBC

Arsenal na duba yiwuwar dauko dan wasan Brentford, kuma mai tsaron ragar Sifaniya David Raya mai shekara 21. (Athletic - subscription required)

Bayern Munich ma na zawarcin Raya bayan kin amincewa da tayin farko da aka yi. (Guardian)

Kungiyar Chelsea na kokarin sasantawa domin daukar zakakurin dan wasan Paris St-Germain dan gaban Faransa wato Kylian Mbappe, mai shekara 24, inda ta ke fatan kawo shi Stamford Bridge a wannan kakar. (Record)

Dan wasan Manchester United, kuma na gaba a Ingila Marcus Rashford,mai shekara 25, ya ce kafin sabon manajan kungiyar Erik Ten Hag ya fara aiki da su a kakar da ta wuce, har ya fara duba yiwuwar barin kulub din (Athletic - subscription required)

Ana sa ran a yau dan wasan tsakiya na Senegal Sadio Mane, mai shekara 31, zai yi gwajin lafiya da Al-Nassr, bayan amincewa da farashin fam miliyan 24 don dauko shi daga Bayern Munich. (Sky Sports)

Chelsea na da tabbacin za ta yi nasarar daukar dan wasan tsakiya na Faransa mai shekara 21, wato Michael Olise, daga kungiyar Crystal Palace. (90min)

Ta tabbata kungiyar Real Sociedad na zawarcin dan wasan Tottenham kuma na bayan Sifaniya, Sergio Reguilon, mai shekara 26. (Mail)

Arsenal na zawarcin mai kai hari kuma na tsakiyar Ghana Mohammed Kudus mai shekara 22 daga Ajax. (Express)

Arsenal din dai ta nuna sha’awar dauko dan wasa Napoli, mai kai hari na Georgia Khvicha Kvaratskhelia,mai shekara 22. (Football Transfers)

Nottingham Forest na son dauko dan wasan Arsenal kuma mai tsaron ragar Amirka Turner, mai shekara 29. (Athletic - subscription required)

A karo na uku Wolves, ta kammala Shirin siyo dan wasan tsakiya na Ingila mai shekara 19, wato Alex Scott daga Bristol City bayan sun yi watsi da tayin fam miliyan 18. (Givemesport)

Source: BBC