BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Arsenal ta siyo Timber daga Ajax

Jurrien Timber (dama)

Fri, 14 Jul 2023 Source: BBC

Arsenal ta kammala ɗaukar ɗan wasan baya na Ajax, Jurrien Timber kan kuɗi fan miliyan 34.

Ɗan wasan, ɗan asalin ƙasar Netherlands, mai shekara 22 ya sanya hannu kan kwantaragi na tsawon shekaru.

Zai ƙara wa bayan Arsenal ƙarfi, bayan da ɗan wasan baya na Arsenal, William Saliba ya amince da tsawaita zamansa a kulab ɗin da shekara huɗu.

Mai horas da Arsenal, Mikel Arteta ya ce: "Mun yi matuƙar farin ciki da sayen Jurrien. Matashin ɗan wasa ne mai basira."

"Jurrien matashin ɗan wasa ne amma ya samu nasarori masu yawa. Yana da ƙwarewa na zuwa gasanni na duniya fiye da sau ɗaya, kuma ya lashe kofuna a Ajax."

Timber na iya wasa a tsakiya ta baya ko kuma ta gefen dama, kuma a baya an alaƙanta shi da tafiya Manchester United, kuma Bayern Munich ta nuna sha'awar ɗaukansa.

Timber ya ce: "na daɗe ina son Arsenal."

Source: BBC