BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Artur Dias ne zai busa wasan Real da City a Champions League

Referee 610x400 File photo

Mon, 8 May 2023 Source: BBC

Hukumar kwallon kafa ta Turai, Uefa ta nada Artur Dias a matakin alkalin da zai busa wasan Real Madrid da Manchester City.

Ranar Talata Real Madrid za ta karbi bakuncin City a wasan farko a daf da karshe a Champions League a Santiago Bernabeu.

Wannan shine karo na hudu da Dias dan kasar Portugal zai busa wasan Real Madrid a Champions League.

Ya fara alkalancin wasan Real da APOEL Nicosia a cikin rukuni a 2017/18, inda kungiyar Sifaniya ta ci 6-0.

Wasa na biyu da ya ja ragama kuwa shine wanda CSKA Moscow ta ci Real Madrid 3-0 a Santiago Bernabeu a wasan cikin rukuni a 2018/19.

Haka kuma Diaz ne ya busa wasan da Real da Paris St Germain suka tashi 2-2 a Bernabeu a fafatawar cikin rukuni a kakar 2019/20.

Source: BBC