Menu

Assam: Matan Indiya na zanga-zanga kan kama masu yi ma ƙananan yara mata auren wuri

Hoton alama

Tue, 7 Feb 2023 Source: BBC

Daruruwan mata na zanga-zanga a jihar Assam a arewa maso gabashin Indiya bayan da aka kama 'yan uwansu maza karkashin wata doka da ke son rage yi wa kananan 'yan mata aure a kasar.

'Yan sandan jihar sun kama akalla maza 2,400 daga ranar Juma'a zuwa yanzu.

Cikinsu akwai mazaje da 'yan uwan kananan 'yan matan da aka so daura wa auren, har da malaman addinin da ke daura irin wannan auren.

Sai dai 'yan adawa sun kira wannan kokarin "abin takaici", suna cewa ana muzgunawa Musulmin jihar ne kawai.

Amma ministan da ke kula da jihar, Himanta Biswa Sarma ya kare matakin, yana cewa "yakin da gwamnatinsa ke yi" kan da ake yi wa kananan yara da wuri ne kuma bai tsame wata al'umma daga hukunci ba.

A Indiya, doka ta hana daura wa 'yan matan da shekarunsu ke kasa da 18 aure, amma duk da haka ana ci gaba da wannan halayyar, musamman saboda dalilai na al'ada da da kuma talauci.

Gwamnati ta ce akan yi wa 'yan mata biyu cikin 10 aure kafi su cika shekara 18 da haihuwa.

Majalisar kasar ta fara duba yadda za ta sauya dokar aure ta kasar zuwa akalla shekara 21 kafin mace ta yi aure.

Amma a tsakanin Musulmai - wadanda yawancinsu ke yin aure a karkashin dokar da addininsu ya tanadar - inda su kan iya aurar da yarinya da zarar ta balaga.

Tun da aka fara kame-kamen na ranar Juma'a, 'yan uwan mazan da aka kama sun fara zanga-zanga a gaban ofisoshin 'yan sanda.

Yawancin matan na cewa mazan da aka kama su ne ke da karfin ciyar da iyalansu, kuma sun dogara kacokan kansu ne.

Rikici na kara bayyana kan dokar aure a Indiya

A ranar Asabar, 'yan sanda a gundumar Dhubri sun lakada wa masu zanga-zangar duka kuma sun harba musu hayaki mai sa hawaye domin su tarwatsa su, kamar yadda jaridar Times of India ta ruwaito.

'Yan sandan sun kuma tuhumi masu aikata wannan laifi, karkashin doka mai suna Protection of Children from Sexual Offences (Pocso) Act.

Dokar ta tanadi daurin shekara bakwai har zuwa daurin rai-da-rai kuma ba a bayar da beli ga duk wanda aka tuhuma da aikata wannan laifin.

Mista Sarma ya ce fiye da mutum 8,100 aka bayyana sunayensu cikin kararrakin da aka shigar a ofisoshin 'yan sanda, ciki har da iyayen angwaye da malaman addinai da suka jagoranci daura auren.

Ya ce ya bukaci 'yan sanda su dauki matakan ba-sani ba-sabo kan su.

Amma 'yan siyasa masu adawa da gwamnati na cewa gwamnatin na matsawa al'ummar jihar ne kawai.

Ripun Bora, shi ne jagoran jam'iyyar siyasa ta Trinamool Congress Party, ya bayyana matakan a matsayin sauya alkiblar dokar kasa domin cin zarafin jama'a.

Gaurav Gogoi, wani dan majalisa daga jam'iyyar Congress ya bayyana matakin gwamnatin na "burga ne kawai", yana cewa 'yan sanda sun dade suna bincike ba tare da sun dauki matakin da dokar kasa ta tanada ba.

A nasa bangaren Mista Sarma ya ce za a ci gaba da aiwatar da wannan dokar ta hana iyaye yi wa kananan 'ya'yansu mata auren wuri har zuwa shekarar 2016, lokacin da za a gudanar da zabe a majalisar jihar.

Source: BBC