Menu

Aston Villa ta ɗauki Pau Torres

Pau Torres

Thu, 13 Jul 2023 Source: BBC

Aston Villa ta sanar da ɗaukar ɗan wasan bayan Spain Pau Torres daga Villarreal kan kuɗi fan miliyan 31.5.

Torres, mai shekaru 26, ya taka leda a ƙarkashin kocin Villa Unai Emery tsakanin 2020 zuwa 2023.

Mai tsaron bayan wanda ya koma makarantar matasa ta Villarreal a shekara ta 2003, ya taka rawar gani yayin da kungiyar ta kare a matsayi na biyar a gasar La Liga a bara.

Ya buga wa Villareal wasanni 173 , inda ya zura kwallaye 12, kuma ya buga wa Spain wasanni 23.

Torres ya fara bayyana a Villarreal a shekarar 2016, inda ya zama dan wasa na farko da aka haifa a karamin garin Valencian da ya fara taka leda a kungiyar a cikin shekaru 13.

Nan da nan ya kafa kansa a matsayin babban dan wasa a ƙungiyar, inda ya lashe gasar Europa a 2021 karkashin Emery lokacin yana cikin wadanda suka zura kwallaye a bugun fenariti da Manchester United.

Torres ya fara buga wa Spain wasa a shekarar 2019 kuma ya buga wasanni biyu a gasar Euro 2020 da kuma gasar cin kofin duniya ta 2022.

Shi ne dan wasa na biyu da Aston Villa ta dauko a bazara, bayan dan wasan tsakiyar Belgium Youri Tielemans ya zo kyauta daga Leicester City.

Villa ta kare a mataki na bakwai a gasar Premier a kakar wasan da ta wuce, inda ta samu tikitin shiga gasar Europa.

Source: BBC