Aston Villa ta doke Burnley 3-1 a wasan mako na uku a gasar Premier League da suka buga ranar Lahadi a Turf Moor.
Matty Cash ne ya fara ci wa Villa kwallo a minti na takwas da fara wasa, sannan minti 12 tsakani ya kara na biyu a raga.
Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Burnley ta zare ɗaya ta hannun Lyle Foster daga baya Villa ta ƙara na uku ta hannun Moussa Diaby.
Kwallo biyun da Cash ya ci a cikin minti 20 a Premier ya zama dan wasan Villa da ya yi wannan bajintar ta cin kwallaye biyu a waje.
Wanda ke rike da bajintar shi ne Daren Bent a karawa da Arsenal, wanda ya ci kwallo biyu cikin minti 15 a Mayun 2011.
Wasa na biyu a jere da Villa ta yi nasara kenan tun bayan da ta sha kashi 5-1 a wasan farko a gidan Newcastle United ranar 12 ga watan Agusta.
Ranar 20 ga watan Agusta Villa ta doke Everton 4-0, sannan ta je ta ɗura 5-0 a Hibernian a karawar nerman gurbin shiga Europa Conference League.
Ranar Alhamis Villa za ta karbi bakuncin wasa na biyu da Hibernian a karawar neman gurbin shiga Europa Conference League.
Daga nan Villa za ta je Anfield, domin buga wasan mako na huɗu a gasar Premier League da Liverpool.