Ranar Lahadi ne Real Madrid za ta ziyarci Atletico Madrid, domin buga wasan hamayya a gasar La Liga fafatawar mako na 26.
Kungiyoyin biyu sun fuskanci juna fiye da sauran masu buga La Liga tun daga kakar 2013/14, kuma wasa na 30 da za su kece raini a tsakaninsu.
A karawar farko a La Liga da za su fafata a bana ranar 12 ga watan Disamba, Real ce ta yi nasara a gida da ci 2-0.
Sauran fafatawar sun kara a Copa del Rey karo hudu da wasa uku a Spanish Super Cup da gumurzu daya a European Super Cup.
Tun daga wasan European Super Cup a Agustan 2018, Real ta yi nasara a wasannin hamayya shida, kuma ba a doke ta ba.
Ciki har da wanda Real Madrid ta lashe Spanish Super Cup a Jeddah a Janairun 2020, bayan da ta yi nasara a kan Atletico a bugun daga kai sai mai tsaron raga.