Menu

Barcelona ka iya karewa a gasar Europa a bana

27736814 Xavi

Fri, 14 Oct 2022 Source: BBC

Barcelona na kan gabar fadawa gasar Europa daga Champions karon farko cikin shekaru 19. A wasanni hudu da kungiyar Barcelona ta buga a Champions ta ci daya ta kuma yi canjaras daya an doketa sau biyu. Rashin nasarar da Barcelona ta yi a San Siro a makon jiya, ya sa Barcelona ta kwana da sanin cewa babu abin da take bukata a wasa na biyu tsakaninta da Inter sai nasara matukar tana son fitowa daga rukunin C, yayin da kungiyoyin da ke da maki kuda tarihin nasarar tsakaninsu ya rabasu. Canjaras din da aka yi ya kara bai wa Inter damar zama a matsayi na biyu, tana biyewa Bayern Munich da ke matsayi na daya, wadda ta samu tsallakwa daga wannan rukuni. Damar da Barcelona ke da ita na fitowa daga rukunin ta ta'allaka ne da rashin nasarar Inter Milan da ke samanta, ko da Barcelona ta ci duka wasanninta matukar ba a yi nasara a kan Inter ba. Ita kuma kungiyar ta Italiya na bukatar nasara daya da canjaras daya ne domin fitowa daga wannan rukuni. Yayin da Viktoria Plzen ta gaza samun ko maki daya a wasanninta. Daga Barcelona har Inter Milan za su fafata da Bayern Munich da ke saman wannan rukuni, abin da ya sanya masana ke kallon cewa ba za a san maci tuwo ba a wannan rukuni sai miya ta kare. Kocin Barcelona Xavi yace akwai bukatar 'yan wasan kungiyar suy kara "matse kaimi" wajen cimma abin da suke bukata. Sakamakon wasan da za a buga tsakanin Barcelona da Bayern Munich a ranar 26 ga watan Oktoba shi ne zai fayyace matsayin kowa a wannan rukuni. Inter Milan za ta buga wasanta da Munich ne a ranar 1 ga watan Nuwamba mai kamawa.

Source: BBC