Yayin da ake ci gaba da gwabza faɗa a birnin Khan Younis da kuma arewacin Gaza, wani bidiyo a shafukan sada zumunta ya nuna yadda dakarun Isra'ila suka tsare wasu Falasɗinawa bayan yi musu tsirara.
Bidiyon, wanda BBC ta tabbatar da gaskiyar sa, ya nuna yadda mutanen ke sanye da gajerun wanduna bayan cire kayan jikinsu, yayin da dakarun Isra'ila ke tsare da su.
Ana tunanin cewa an kama mutanen ne a garin Beit Lahia da ke maƙurar arewacin Zirin Gaza.
Lokacin da aka tambayi mai magana da yawun gwamnatin Isra'ila, ya shaida wa BBC cewar dukkanin mutanen manya ne waɗanda suka kai shekarun aikin soji, kuma an kama su ne a "wurin da ake sa ran fararen hula sun gudu daga nan tun makonnin da suka gabata."
Bidiyon ya nuna gomman mutanen a kan layi, wanda ke nuna cewa an umarce su da su cire takalma, waɗanda ake iya gani baja-baja a kan titi.
Sai kuma dakarun Isra'ila da motoci masu sulke da ke gadin su.
Wasu hotunan sun nuna yadda aka ɗauke su a motocin soji.
Kafofin yaɗa labaru na Isra'ila sun bayyana mutanen a matsayin mayaƙan Hamas waɗanda suka miƙa wuya.
Akwai kuma wani hoton, sai dai BBC ba ta tantance shi ba, wanda ke nuna wasu mutane da aka ɗaure musu idanu da ƙyalle, rusune a ƙasa.
Rundunar sojin Isra'ila ta IDF dai ba ta ce komai ba game da hotunan, sai dai mai magana da yawunta, Daniel Hagari ya faɗi a ranar Alhamis cewa "Mayaƙan Isra'ila sun tsare tare da yi wa ɗaruruwan mutanen da ake zargin ƴan ta'adda ne tambayoyi."
"Da dama daga cikin su sun kuma kai9 kansu ofishinmu cikin kwana ɗaya da ya gabata. Ana amfani da bayanan da aka samu daga gare su wajen yakin da ke gudana."
Ranar Juma'a, mai magana da yawun gwamnatin Isra'ila, Eylon Levy ya shaida wa BBC cewar an tsare mutanen ne a Jabalia da Shejaiya da ke arewacin Gaza, wanda ya bayyana a matsayin "yankunan da Hamas ke da ƙarfi."
"Ana magana ce ta mutane matasa waɗanda aka gano a yankin da ake sa ran fararen hula sun tsere daga wurin tun makonnin da suka gabata," in ji shi.
Mista Levy ya ƙara da cewa za a yi musu tambayoyi "domin gano ko su wane ne a cikin su ƴan ƙungiyar Hamas da kuma waɗanda ba ƴan ƙungiyar ba ne."
Ya jaddada cewa mutanen da aka tsare ɗin an kama su ne a wuraren da dakarun Isra'ila suka yi artabu da Hamas. Sun "riƙa yin shigar-burtu suna nuna tamkar su fararen hula ne" kuma suna ayyukansu ne a cikin gine-gine na fararen hula.
Sai dai bayanai masu cin karo da juna na fitowa daga mutanen da har yanzu suke a yankin.
Wakilin sashen Larabci na BBC, Ethar Shalaby ya yi magana da wani mutum wanda ya ce ƴan'uwansa 10 na cikin mutanen da mayaƙan Isra'ila suka tsare ranar Alhamis a Beit Lahia.
Yana jin tsoron abin da zai iya faruwa gare shi da iyalansa, saboda haka ba ya son a ambaci sunansa.
Yana zaune ne a wani yanki na Gabas ta tsakiya.
Ya ce ƴan'uwansa su biyu sun kira shi da misalin ƙarfe biyu na rana, agogon Gaza.
Sun faɗa masa cewa dakarun Isra'ila na tsare da ƴan'uwansa 10.
Ƴan'uwansa da ya yi magana da su sun shaida masa cewa dakarun Isra'ila sun shiga yankin ne inda suka yi amfani da lasifika suka sanar da mutanen cewa su fito daga gidajensu da kuma makarantu na Majalisar Dinkin Duniya.
Sun faɗa masa cewa sojojin na Isra'ila sun umurci mata su tafi asibitin Kamal Edwan.
Daga nan suka yi barazanar harbe matan matuƙar mazan ba su fito ba.
Ya ce a yanzu ya samu labarin an saki guda bakwai daga cikin ƴan'uwan nasa sun koma gida.
Sai dai bai san makomar sauran ƴan'uwansa huɗu ba waɗanda ke hannun dakarun na Isra'ila.
Ɗaya daga cikin ƴan jarida mafi suna a Gaza, Diaa al-Kahlout, wanda wakili ne na kafar yaɗa labaru ta Araby al-Jadeed na daga cikin waɗanda aka tabbatar cewa ana tsare da su.
Kafar, wadda ke yaɗa labaru a harshen Larabci da kuma turancin Ingilishi ta ce sojojin Isra'ila sun kama Mista al-Kahlout tare da ƴan'uwansa da wasu fararen hula a Beit Lahia.
A ranar Alhamis, kafar yaɗa labarun ta yi allah wadai da da abin da ta kira tsarewa na "cin zarafi" da ake yi wa Mista al-Kahlout.
Ta ƙara da cewa sojojin sun tursasa wa mutanen su cire kayan da ke jikinsu, sannan suka riƙa yi musu "binciken ƙwaƙwaf a lokacin da suka kama su, kafin aka tafi da su zuwa wani wuri da babu wanda ya sani."
Kafar ta yi "kira ga ƙasashen duniya da masu kare haƙƙin ƴan jarida da ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama su yi tir da wannan cin zarafi "da Isra'ila ke aikatawa a kan ƴan jarida na yankin.
BBC ta tambayi rundunar sojin Isra'ila da IDF game da labarin tsare Mista al-Kahlout.