BBC na neman zaƙaƙuran 'yan jaridar Afirka da za ta ɗaga sama, domin shiga gasar Komla Dumor ta wannan shekarar, kuma shi ne karo na ta takwas a jere da ake yin wannan gasa.
Ana gayyatar 'yan jarida daga sassa daban-daban na duniya domin shiga wannan gasa, da nufin gano matasan 'yan jarida masu hazaƙa a nahiyar.
Wanda ya yi nasara a wannan gasa ta 2023, zai samu nasarar shafe watanni uku ya na aiki a hedikwatar BBC da ke birnin Landan, domin sanin makamar aiki ta fannoni daban-daban.
Za dai a rufe shiga gasar, ranar 14 ga watan Faburairu 2023, da misalin karfe 11:59 agogon GMT.
An kirkiri gasar ce domin tunawa da kuma girmama ɗan ƙasar Ghana Komla Dumor, fitaccen mai gabatar da shirye-shirye a tashar labarai ta BBC, wanda ya yi mutuwar fuju'a a shekarar 2014, a lokacin yana da shekara 41 a duniya.
Mai dakin marigayin, Kwansema Dumor ta shaidawa Victoria Rubadiri da ta yi nasarar lashe gasar a shekarar 2020, cewa ta na ''alfahari da rawar da mijinta ya taka a BBC'', sannan ita da iyalanta su na miƙa sakon godiya ga BBC da suke tunawa da mijinta ta wannan fanni na sanya kyauta saboda shi.
BBC dai na bai wa 'yan jaridar Afirka kwarin gwiwar shiga gasar, wadda manufarta shi ne fitar da zaƙaƙurin ɗan jarida, da zai sake koyon aikin da zai daukaka shi a nahiyar.
Sannan ɗan jaridar da ya yi nasara, zai samu horo, da ziyartar wata kasa a Afirka domin yin rahoton da ya yi bincike a kai sannan za a yada shi a tashar BBC duk duniya su kalla.
Dumor ya yi fice a Afirka, wajen salon aikin shi na jarida, da yadda ya ke gabatar da shiri da rahotanni cikin ƙwarewa da basira, haƙiƙa aikinsa ya shafi Afirka da ma duniya baki ɗaya.
BBC na son ci gaba da yin wannan gasa a kowacce shekara, domin taimakon 'yan jarida, yadda za su bada labarin da ya shafi Afirka domin duniya ta san da su.
Dan jarida na kasar Zambia, Dingindaba Jonah Buyoya ne ya lashe gasar a bara kuma mutum na farko daga kudancin Afrika.
A lokacin horon da ya samu, ya je Seychelles domin yin rahoto a kan yadda tsirrai a cikin teku za su taimaka wajen yaki da sauyin yanayi.
"Komla Dumor ya kara min kwarin gwiwa kuma lashe wannan gasar abin alfahari na ne," in ji Buyoya.
"Ina kira ga 'yan jarida na Afrika su shiga wannan gasar domin samun kwarewa wajen yin labaran da suka shafi Afrika."
Daraktar sashen turanci na BCC, Liliane Landor, ta ce: "Na yi farin ciki da BBC ta kirkiro wannan gasa saboda Komla Dumor, a kuma ga irin abin alfaharin da ya bari, ina farin cikin dawo da gasar nan, ga shi har an shiga shekara ta bakwai.
Dumor dai shi ke gabatar da wani shiri irinsa na farko da BBC ta fara, da kacokan ya maida hankali kan labaran da suka shafi Afirka, wato Focus on Africa, da ake gabatarwa a Talbijin da harshen turanci.
Kuma shi ne ɗaya daga cikin masu jagorantar gabatar da shirin safe da ya shafi Turai.
A shekarar 2007 ya fara aiki da BBC, bayan shafe shekara 10 ya na gabatar da shiri da harshensa na gida wato Ghana, ya kuma taba cin kyautar ɗan jaridar shekara na Ghana.
Tsakanin shekarar 2007 zuwa 2009, ya fara gabatar da shirin "Network Africa" da sashen turanci na BBC, kafin daga bisani ya koma fannin shirye-shirye na "The World Today" duk dai a BBC.A shekarar 2009, Dumor ya zama na farko da ya fara gabatar da labaran kasuwancin Afirka, wato African business da ake yadawa a tashar BBC.
Ya yi tafiye-tafiye a nahiyar Afirka, inda ya rinƙa haɗuwa da manyan 'yan kasuwar Afirka, da dauko rahotannin abubuwan da ke faruwa ta fannin kasuwancin Afirka, a lokacin da suke cin kasuwarsu a duniya.
A shekarar 2013, Dumor ya fito da shahararriyar mujallar nan ta Afirka wato "New African magazine", wadda ta ke fitar da shahararrun mutanen nahiyar guda 100, kuma Komla na daga cikinsu.
Wadanda suka lashe gasar a baya: