0
MenuAfrica
BBC

Ba kotu ya kamata ta tantance wadanda suka ci zabe ba – Jonathan

Tue, 13 Apr 2021 Source: bbc.com

Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya yi kira da a karfafa dokokin zaben kasar ta yadda takardar kada kuria kawai za ta tantance wadanda suka yi nasara a zabe, ba kotu ba.

Mista Jonathan ya jaddada cewa abin da aka saba a kai shi ne alhaki ya rataya a kan hukumomin zabe wajan dawo da 'yan takara da bayyana wadanda suka yi nasara yayin da bangaren shari'a ke cikawa ta hanyar tabbatar da sakamakon da aka bayyana ko soke zaben da aka yi ba dai-dai ba da kuma ba da umarnin a sake zaben.

Ya ce : "Na riga na yi bayani a bainar jama'a a kan hakan don cewa takardar jefa kuri'a ba bangaren shari'a ba ne zai tantance wanda zai ci zabe ko kuma ya zabi shugabannin siyasa. Kamata ya yi takardar zaben ta kasance ita kadai ce tushen zabar shugabannin siyasa. "

An shigar da kararraki da dama a gaban kotu a kan lamuran da suka shafi fafatawa a tsakanin jam'iyyun.

A baya kotun koli ta soke zaben Emeka Ihedioha na jam'iyyar PDP a matsayin gwamnan jihar Imo .

Kotun ta kuma bayyana Hope Uzodinma na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya yi nasara a zaben da aka yi a ranar 9 ga watan Maris na shekarar 2020.

Source: bbc.com